Kwanan baya, shugabannin manyan kungiyoyi da cibiyoyin tattalin arziki na duniya sun kawo ziyara ta musamman kasar Sin, inda suka gana da Shugaba Xi Jinping na kasar. Daga cikin tawagar akwai shugabar bankin duniya, Ajay Banga, da darekta-janar ta kungiyar cinikayya ta duniya, Ngozi Okonjo-Iweala. Haka nan, akwai shugaban bankin raya kasashe a karkashin kawancen BRICS, Dilma Rousseff, da kuma manajan darektar asusun ba da lamuni na duniya, Kristalina Georgieva.
Wadannan kusoshin na tattalin arziki sun yaba da yadda kasar ta zama madubin dubawa a bangaren tsamar da al’umma daga kangin talauci da sabbin salonta na bunkasa tattalin arziki, kana da irin tallafin da ta dade tana bayarwa ga bunkasa ayyukan kungiyoyin tattalin arzikin duniya.
- Dangote Ya Musanta Labarin Ciyo Bashin NNPC Na Dala Biliyan 1 Domin Tallafa Wa Matatarsa
- Yaƙin Gaza Ya Kusan Zuwa Ƙarshe – Amurka
Hakika, kasar Sin ta jima tana taka rawar gani a janibin raya tattalin arzikin duniya kuma ta sha alwashin ci gaba da zama kashin bayan duniya ta fuskar samar da damammaki da cin moriyar juna a tsakanin kasashen duniya ba tare da nuna bambanci ba.
Sakamakon yadda kasar Sin take samun gawurtar tattalin arziki cikin hanzari fiye da shekaru 40 da ta yi da fara bude kofa, hakan ya sa ta hau turbar samun ci gaba mai inganci, kuma duk da haka har yau ba ta zauna ba, tana kara bullo da gyare-gyare masu zurfi don tabbatar da dorewarsa. Wannan himma ta kasar Sin, ta taimaka wa habakar tattalin arzikin duniya da a kalla kashi 30 cikin dari.
Wani rahoton bankin duniya a shekarar 2022 ya bayyana cewa, daga shekarar 2013 zuwa 2021, kasar Sin take da kimanin kashi 38.6 cikin dari na ci gaban tattalin arzikin duniya. Wannan ya nuna tagomashin da Sin ta kara wa tattalin arzikin duniya ya fi na dukkan hamshakan kasashe mafi bunkasar tattalin arziki na kungiyar G7, inda hakan ya sa kasar ta tsere wa kowa wajen habaka tattalin arzikin duniya.
Ba da fatar baki ne kasar Sin ta zama haka ba, a aikace ne, domin ko a watan Oktoban da ya gabata, bayanan da Hukumar Kididdiga ta Kasar Sin ta fitar sun nuna cewa karfin hada-hadar tattalin arzikin kasar Sin (GDP) a rubu’i na uku na shekarar 2024, ya kai Yuan tiriliyan 94.97, watau kimanin Dala tiriliyan 13.09, wanda yake nuna kasar ta samu karin ci gaba da kashi 4.8 a mizanin shekara-shekara.
Duk da cewa, har yanzu kasar Sin ba ita ce ta farko ba a jerin kasashe mafi karfin tattalin arzikin duniya, ita ce ta biyu, hakan bai sa ta zama marowaciya ba, ta bullo da kawance daban-daban na cin moriyar juna kamar su shawarar “ziri daya da hanya daya” (BRI), dandalin kawancen Sin da Afirka na FOCAC da sauransu. Zuwa yanzu, kasar Sin ta rattaba hannu a yarjejeniyoyin hadin gwiwa a karkashin BRI da fiye da kasashe 150 da kuma manyan kungiyoyin duniya guda 30.
Bugu da kari, wasu bayanai daga ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin sun nuna cewa, zuwa karshen shekarar 2023, kamfanonin kasar Sin sun kafa rassa kimanin 17,000 a kasashen da suka rattaba hannu a shawarar BRI. Wadannan kamfanonin, sun zuba jari kai-tsaye na fiye da Dala biliyan 330, baya ga samar da ayyukan yi a cikin gida a kalla 530,000 daga sassan kawancen tattalin arziki da cinikayya da aka kulla a karkashin shawarar.
Wadannan duka misalai ne da suke nuna yadda tattalin arzikin kasar ke ci gaba da zama bango majinginar duniya kuma kamar yadda Shugaba Xi Jinping na kasar ya alkawarta, kasar za ta ci gaba da bude kofa ga sauran kasashe da tafiya a kan manyan ingantattun dokokin cinikayya na duniya domin cin gajiyar juna. (Abdulrazaq Yahuza Jere)