Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa, sannu a hankali tattalin arzikin Nijeriya na farfaɗowa, yana mai alaƙanta cigaban da aka samu da sauye-sauyen da gwamnatin sa ke aiwatarwa a sassa daban-daban.
Shugaban ya bayyana haka ne a garin Yenagoa na Jihar Bayelsa a ranar Alhamis a jawabin sa na buɗe babban taron shekara na Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE).
- EFCC Ta Gurfanar Da Tsofaffin Gwamnoni Da Tsofaffin Ministoci, Bayan Kwato Kadarorin Biliyoyin Naira A Kasashen Waje
- An Kama Wasu Ƴansanda Kan Zargin Kisan Ɗalibin Jami’ar Kwara
Da yake magana ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, Shugaba Tinubu ya ce ya shafe watanni goma sha takwas da suka gabata yana kafa harsashin samar da Nijeriya mai arziki.
Ya ce: “Ina farin cikin sanar da ku cewa ta hanyar gyare-gyaren mu, muna ganin tattalin arzikin mu yana farfaɗowa. A yau, biyan ɗin bashin da muke yi da kuɗin shiga ya sauko sosai daga kusan kashi 100 zuwa kusan kashi 65.
“An shafe watanni goma sha takwas da suka gabata wajen aza harsashin wannan kyakkyawar manufa ta samar da cigaban Nijeriya.
“Wannan shi ne abin da Ajandar Sabunta Fata ke tattare da shi – wato sake farfaɗo da imani da fatan dukkan ‘yan Nijeriya kan yadda ƙasar su za ta bunƙasa da kuma samar da yanayin da zai bai wa kowa da kowa a cikin ta damar bunƙasa.
“Amma mun fahimci cewa akwai wasu manyan cikas da ke kan hanyar fito da ɗimbin abubuwan da Nijeriya ke da su. Kuma mun yi amfani da lokaci da kuzari kuma mun mai da hankali wajen magance waɗannan.
“Biyu daga cikin manyan abubuwan da suka fi muhimmanci sanannu ne a gare ku: tsarin tallafin man fetur wanda ya hana mu samun biliyoyin daloli a duk shekara da za a iya saka hannun jari da su a muhimman abubuwan more rayuwa, da tsarin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje wanda za a iya amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba.”
Ya bayyana cewa sakamakon gyare-gyaren da aka yi, kuɗaɗen shiga na dukkan matakai uku na gwamnati – wato Tarayya, Jihohi, da Ƙananan Hukumomi – ya samu bunƙasa sosai, wanda hakan ya ba da damar saka hannun jari a fannin ayyukan jinƙai, samar da ababen more rayuwa, da samar da tsaro.
Shugaban ya bayyana cewa hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke na bai wa ƙananan hukumomi ’yancin cin gashin kan su, bayan ƙarar da Gwamnatin Tarayya ta shigar, yana da nufin ƙarfafa harkokin mulki a matakin ƙananan hukumomi da kuma samar da cigaba.
Shugaba Tinubu ya jaddada kuɗirin sa na ganin Nijeriyar da ba a bar wani ɗan ƙasa a baya ba a cikin talauci ko cuta wanda hakan na jawo mutuntawa a duniya.
Ya ce: “An fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na naira 70,000 a dukkan ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, inda da yawa daga cikin gwamnatocin jihohi suka ƙudiri aniyar aiwatar da hakan. Sama da ɗalibai 46,000 ne ke cin gajiyar asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya a faɗin manyan makarantu 59 da sama da naira biliyan 5. Kashi na farko na ma’aikatan gwamnati 500,000 ne za su ci gajiyar shirin bayar da lamuni na masu amfani da naira biliyan 100.
“Yayin da man fetur ya kasance babbar hanyar samun kuɗaɗen shiga ga Nijeriya, muna zuba jari sosai a wasu ɓangarori don bunƙasa tattalin arzikin mu don samun cigaba mai ɗorewa.
“Ƙaddamar da shirin Shugaban Ƙasa kan iskar gas (CNG) dabara ce don yin amfani da albarkatun iskar gas ɗin mu don rage tsadar sufuri da kusan kashi 60 da kuma samar da yanayi mai tsafta da lafiya ga ‘yan ƙasa. Wannan yunƙurin ya samar da kusan dala miliyan 200 na jarin kamfanoni masu zaman kan su a cikin shekara ɗaya da ta gabata.”
Ya ce kowane ɗaya daga cikin shirye-shiryen an tsara shi ne domin ya zama wani aiki da zai samar da cigaba mai ɗorewa a rayuwar miliyoyin ‘yan Nijeriya.
Yayin da yake yaba wa kafafen yaɗa labarai kan sadaukar da kai ga gina ƙasa, musamman wajen tallafa wa dimokuraɗiyyar Nijeriya, Tinubu ya jaddada cewa ayyukan gwamnati da na kafafen yaɗa labarai na da alaƙa da juna, kuma dukkan su suna da matuƙar muhimmanci wajen amfanar da jama’a.
Ya ce: “Haka zalika, ya zama wajibi kafafen yaɗa labarai su riƙa tuntuɓar waɗanda aka zaɓa da waɗanda aka naɗa, da kuma tabbatar da cewa muna gudanar da ayyukan mu ta hanyar da za ta ƙarfafa dimokiraɗiyya – ba ta raunana ta ba. Wannan muhimmin aiki kuma dole ne a yi shi cikin mutunta juna da haɗin kai, ba wai ƙyama da adawa ba; wannan daidaitawar tana ba mu damar cimma manufofin gamayya da ke amfanar al’umma gaba ɗaya.”