Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya nemi masu zuba jari na ciki da wajen kasa su rungumi Nijeriya a mastayin fagen su na zuba jari, ya kuma ce, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shirya samar wa ‘yan kasuwa yanayin gudanar da kasuwanci mai riba a kasar nan.
Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan kiran ne ranar Litinin a yayin da ya karbi bakunci shugabannin kamfanonin ‘First Surat Group’ da na ‘MTN Nigeria’ a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Henry Kissinger, Ya Mutu Yana Da Shekaru 100
- Tinubu Zai Sake Karbo Sabon Bashin Dala Biliyan 8.69
Ya kuma nemi ‘MTN Nigeria’ ta ta jagoranci fara amfani tare da wayar da kan al’umma a kan hanyoyin mu’amala da ‘Digital mobile money’.
Mai magana da yawun shettima, Stanley Nkwocha, ya sanar da haka a takardar manema labarai da aka raba a Abuja, ya ce, wannan gwamnatin za ta yi aiki da kowa don samar wa da al’umma aikin yi.
Tun da farko shugaban kamfanin ‘First Surat Group’, Dakta Ali Maina, ya ce, kamfanin ya zuba jarin miliyoyin naira don bunkasa jin dadin al’ummar Nijeriya, a nasa martanin, shugaban kamfanin ‘MTN Nigeria’, Ernest Ndukwe ya ce kamfanin ya kuduri aniyar tallafa wa shugaban kasa Tinubu wajen cimma kudurinsa na ‘Renewed Hope Agenda’.