• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tattauna Sirrinki Da Mijinki

by Amina Usman
2 years ago
Mijinki

Aure wani babban al’amari ne wanda ubangiji ke hada zukata da ruhi waje daya, aure aka ce Bautar Ubangiji, Aure Raya Sunna.

Idan muka dubi irin yadda aka yi wa aure kirari a farkon rubutu za mu gane cewa aure babban al’amari ne. A duk sanda maganar aure ta kullu tsakanin mace da namiji, to akwai wasu abubuwa da za a yi dubi da su wanda wadannan lamura suke kara danko da kuma karfafuwar alaka mai karfi tsakanin miji da mata, a wani bangaren kuma hakan kan kasance matsala tsakanin ma’auratan biyu.

  • Peng Liyuan Ta Gana Da Uwargidan Shugaban Zambia

Sirri: Tabbas sirri a gidan aure yana taka mahimmiyar rawa, kama daga kan miji har zuwa kan ‘yan uwa da kuma dangi. Amma maudu’i mu na yau zai karkata ne ga bayyana sirri ga miji hakan yana da fa’ida ko kuwa akasin haka?

Uwargida, daga ranar da kika ce kin ji kin gani kin amince za ki aure wane to fa ya kamata ki sani cewa dole akwai wasu lamuran rayuwarki da ya kamata a ce mijinki shi ne kan gaba. Kamar misali, bari mu fara da mata masu sana’ar kasuwanci. Idan uwargida ta kasance tana harkar kasuwa da ma an san cewa dole harkar kasuwa akwai hulda da wasu nau’i na maza walau ko wanda kike sarar kaya a hannunsa ko kuma dan aiken dake miki kai kawo a harkar kasuwanci, uwargida idan fa kika sake kina ayyukanki gaba gadi ba kya labarta masa halin da ake ciki dole shakku zai shiga tsakani saboda a kullum zai ga kina mu’amala wanda shi bai san da su ba ko kuma ba a shawarce shi ba.

Duk duniya in aka dauke iyaye babu wanda ya kamata a ce abokin shawara ne ga uwargida sai miji.

LABARAI MASU NASABA

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

Mata da yawa in aka ce tattauna sirri da miji suna dauka cewa su zo su baje sirrin abin da ke faruwa agidan iyayensu shi ake nufi, to ba haka abin yake ba ko kusa, sirrin gidan iyaye ba abu ne da za ki fito ki dinga yadawa ba. sirrin gidanku ya kasance na gidanku ne kawai.

Tattauna sirri da miji hakan kan sa maigida ya kasance yana ganin girma dakuma kimar matarsa saboda tana kokarin fayyace masa dukkan lamura.

Bayyana sirri ga miji yana rage yawan zarge-zarge da ke faruwa a gidajen aure, saboda za mu ga cewa idan uwargida ta kasance mai bayyana lamurranta ga miji hakan zai sa ko da wani zance ya bullo ba zai yi saurin daukar fushi ba. Yanzu kamar matan da mazajensu ke sanya musu ‘yan leken asiri ai rashin bayyanawa miji sirri shi yake jawo haka.

Bayyana sirri ga maigida hakan kansa miji ya kasance ko da a ce ba duka yake gaya miki ba amma dai a kalla za ki san wasu abubuwa da dama daga cikin nasa lamuran.
Uwargida ta kasance mai sakin sirrinta ga miji ya kan sa wani lokaci a sami kyakkyawar alaka da fahimta wanda da wuya ka ga an yi rikici.

Kar uwargida ta ce ai nima baya gaya min damuwarsa saboda haka nima ba zan gaya masa tawa ba, to Hajiya kin yi kuskure, saboda da ma a zamanku shi ne babba saboda haka ke ya kamata ki kwantar da wuya akan haka.

Idan uwargida ta kasance sirrinta tana koka wa mijinta hakan na kara sawa ya ji tausayinta sosai. yanzu sai ka ga mace ta shiga adashe ya fi kashi uku kuma fa ba ta da sana’a sai ‘yan kame-kame da haka take samu ta yi zubi, mijinta kuma bai sani ba to fa duk ranar da ta charle kudin zubi ya gagara aka zo aka tsaya mata akai dole wannan lamari ya jawo fada da matsala tsakanin ma’aurata amma kin ga in uwargida ta kasance mai bayyana wa miji sirri kafin a kai ga an zo an tsaya ana mai da zance sai ki ga ta lallabi dan mijinta ta samu ya yi mata zubi hankali kwance.

Wani mijin ba zai taba sanin me matar shi take ciki ba sai ta kwaye mata sannan za ta yi kokarin sanar masa wanda hakan kuskure ne.

Irin mata masu tara kaya da kudin mutane a kansu a yi ta rikici miji bai sani ba, wasu matan saboda rikici har hukuma za ki ga an kira musu wanda idan ba mai bayyanwa miji sirri bace kin ga daga nan an sami matsala. Rashin gaya wa miji sirri kan sa miji ya koyi bakin hali da rashin sakin fuska.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

October 12, 2025
tusar gaba
Adon Gari

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

August 31, 2025
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
Ado Da Kwalliya

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

August 3, 2025
Next Post
Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Baje Kolin Sin Da ASEAN Karo Na 20

Firaministan Sin Ya Halarci Bikin Bude Baje Kolin Sin Da ASEAN Karo Na 20

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

October 16, 2025
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

October 16, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

October 16, 2025
Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.