Mai Martaba Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Neja, ALHAJI YAHAYA ABUBAKAR, da ya zama Etsu Nupe a ranar 13 ga watan Satumbar 2003, ya cika shekara 20 cif a gadon sarauta a ranar 11 ga Satumbar 2023. LEADERSHIP ta tattauna da shi a lokacin da ake shirye-shiryen bikin cika shekara 20 da ba shi sandar girma. Sani Anwar ya fassara tattaunawar kamar haka:
Mai martaba, me ‘yan Nijeriya za su yi tsammanin gani a bikin cikarka shekara 20 cif a gadon sarauta?
Muna yi wa Allah SWT godiya da ya nuna mana wannan lokaci na cika shekara 20 kan garakar mulki, wanda muka gada daga iyaye da kakanni, wadda ake yi wa lakabi da sarautar Kasar Etsu Nupe a ranar 11 ga watan Satumbar 2003… don haka muna yi wa Allah Madaukakin Sarki godiya da ya azurta mu da wannan baiwa, ba don wayonmu ko iyawarmu ko mun fi wani ba.
Wani babban abin sha’awa shi ne, yadda lokacin haihuwata ya fado a ranar 12 ga watan Satumba. Domin an haife ni a ranar 12 ga watan Satumbar 1952, wannan ya sa muke hade bukukuwan wuri guda tare da yi wa Allah (SWT) godiya. Kamar yadda muka tsara, a ranar 11 da 12 za mu ziyarci gidajen yari, gidajen marayu da asibitoci, domin karfafa masu gwiwa su kara yin imani da Allah Madaukakin Sarki, sai kuma sauran wasu gurare masu muhimmanci daga ranar 11 zuwa 13 ga wata.
Sannan a ranar 14 ga wata, akwai shirye-shirye da muka yi na tallafa wa marasa karfi da kayan sana’o’i, jari ga masu karamin karfi da sauran makamantansu. Don haka, muna so mu yi amfani da wannan dama wajen isar da sakonmu, musamman ga masu rauni ko kananan sana’o’i kan wannan kudiri namu na taimaka masu da abin da ya shafi harkokin kudi da kuma kayan abinci.
Har ila yau, akwai addu’a ta musamman da za a yi, domin kara yin godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Ranar Asabar kuma, za mu fito mu bayyana wasu daga cikin ‘ya’yanmu maza da mata da muka bai wa sarautun gargajiya tare da kaddamar da littafin tarihin Kasar Nupe da kuma kafatanin sarakunan da suka mulki kasar. Muna so mu kaddamar da wannan littafi, domin al’umma su yi amfani da shi don sanin wane ne Nupe, yaya kuma yake gudanar da rayuwarsa. Babu shakka, wannan littafi ya hada abubuwa da dama da suka hada da al’adu da sauran rayuwarmu kacokan.
Wane irin farin ciki za ka bayyana na kwashe tsawon shekara 20 kan wannan mulki?
Alhamdu lillah, ina yi wa Allah SWT matukar godiya. Na samu kaina a matsayin sarki ba tare da na tsarawa kaina haka ba, don haka ina yi wa Allah godiya da na samu kaina a cikin sarautar gargajiya kuma guda cikin sarakunan wannan kasa. Kamar yadda aka sani ne, dukkanin wanda ya gaji sarauta ba shi da burin da ya fi na zama sarki, amma abin tambayar shi ne yaya zai zama kuma yaushe? Shi ne abin da babu wanda ya sani sai Allah madaukakin sarki, domin kuwa abin a hannunsa yake, cikin mutane da dama amma Allah ya zabo ni ya ba ni ragamar wannan mulki.
Saboda haka, a matsayinmu na shugabanin al’umma, ana kyautata mana zaton yin abubuwan da suka dace tare da tabbatar da ganin al’umma sun kaunaci juna, sun kuma zauna cikin aminci da kwanciyar hankali a gidajensu da wuraren sana’o’insu da kuma gonakinsu, musamman ganin yadda mafi yawansu manoma ne. Kazalika, muna da babban kogi, Kogin Neja, wanda ke kwaranya tun daga yankin kudu zuwa arewa ko daga yankin arewa zuwa kudu kai tsaye zuwa kan iyakarmu. Babu shakka Allah ya albarkace mu, ga kuma kasar noma wadda duk abin da muka shuka yana fitowa. Shi yasa nake son karfafa gwiwar al’ummarmu wajen ganin sun sake rungumar wannan noma, domin ba abu ne da ake yin sa da baki ba, abu ne da ake yin sa a aikace. Sannan, muna sake jan hankalin manoma, mu rungumi wannan noma da kanmu, domin karfafa wa mutane gwiwa wajen yin wannan noma, domin idan kana so mutane su yi abin da ya kamata, dole ne sai ka nuna musu yadda za su yi. Saboda haka, wajibi ne mu yi abin a aikace ta yadda sauran mutane za su gani su ma rungume shi su yi.
Haka nan, idan aka dubi bangaren ilimi, nan ma dole a sara mana, domin kuwa babu wani abu da muke yi cikin jahilci ba tare da ilimi ko sani ba a cikin al’ummarmu. Haka zalika, babu wani ci gaba da za a samu idan ya kasance babu ilimi a ciki, shi yasa a koda-yaushe muke ci gaba da karfafar ilimin firamare da na sakandire tare da jajircewa wajen ganin an ingata su. Muna da namu makarantun firamaren, sannan mun kafa makarantun sakandire, muna kuma yin alfahari da gina Jami’a tamu ta kanmu mai zaman kanta, domin karfafa wa abin da gwamnatinmu take yi mana a wannan fanni na ilimi.
Ko shakka babu, muna da wannan tsari da ya shafi harkokin ilimi, muna kuma ci gaba da karfafa wa mutane gwiwa wajen bayar da tasu gudunmawar a wannan bangare, sannan muna amfani da kudaden da muka samu wajen daukar nauyin yaranmu a harkar makarantu. Haka nan, mu kan yi gyaran ajujuwan da suka lalace tare da samar da kujerun zama da sauran makamantansu. Muna kuma daukar nauyin dalibai masu hazaka, mu ba su tallafi na musamman don ci gaba da karatunsu zuwa manyan makarantu.
Ba iya nan kadai muka tsaya ba, idan akwai matsalar rashin lafiya, ba ma taba wasa da ita kamar yadda masu magana ke cewa, “lafiyar al’umma ita ce jarinsu”; da zarar an ce babu lafiya, babu wata magana kuma. Wannan dalili ne yasa muke amfani da dan abin da ke hannunmu wajen samar da dakunan sha-ka-tafi da gyaran sauran wuraren kula da harkokin lafiya da kuma samar da magunguna, domin tallafa wa masu karamin karfi. Sa’an nan ba mu yi kasa a gwiwa ba, wajen ci gaba da karfafa tare da habaka makarantun koyon jinya da unguwar zoma, domin yin daidai da na zamani.
Mece ce mahangarka a kan wannan kasa tamu Nijeriya?
Sanin kowa ne cewa, Nijeriya a halin yanzu na fama da kalubale iri daban-daban, amma abin da ya fi ci mata tuwo a kwarya shi ne batun matsalar tsaro, wanda ya addabi kowa da kowa. Koda-yake dai, gwamnati na yin namijin kokari wajen ganin ta shawo kan al’amarin, duk da cewa abu ne wanda ke bukatar gudunmawar kowa da kowa. Ina da yakinin cewa tun daga namu bangaren na sarautar gargajiya, muna da irin gudunmawar da za mu iya bayarwa don taimakon gwamnati. Saboda haka, ya zama wajibi mu koma ga Allah tare da ci gaba da yin addu’o’i, domin samun saukin wannan iftila’i na rashin tsaro a fadin yankunanmu baki-daya.
Har ila yau, lokaci zuwa lokaci mu kan gabatar da shawarwari tare da aikewa da takardu ga Kananan Hukumomi, Jihohi da kuma Gwamnatin Tarayya ta yadda za a magance wannan tsala ta rashin tsaro, wanda ko shakka babu; indai har za a yi amfani da wadannan shawarwari yadda ya kamata, za a kawo karshen wannan takaddama da ta ki cit a ki cinyewa ta rashin tsaro nan ba da jimawa ba. Babu yadda za a yi a lokaci guda ka iya kawar da wannan matsala baki-daya, saboda babu wata kasa tilo a duniya da za a ce ta iya kaucewa ire-iren wadannan matsaloli baki-daya a lokaci guda. Dalili kuwa, matsalolin tsaron wata kasa da ban da na wata. Mu tamu matsalar ta sha ban-ban da ta sauran kasashe ta fuskoki da dama da ya hada da tsoro furgici da kuma fargaba. Saboda haka, akwai bukatar a yi dukkannin abin da ya dace domin kawar da wannan annoba, don ganin al’umma sun dawo cikin hayyacinsu sun ci gaba yin harkokinsu kamar yadda aka saba.
Babban abin haushi da takaici shi ne, yadda wasu abubuwa ke faruwa a Nijeriya fiye da shekaru 40 da suka wuce na wasu masu hana ruwa gudu. Su ne kullum ake kuka da su tare da zargin su cewa, su ‘yan kadan ne amma sun hana ruwa gudu, su ne kadai ke amfana da arzikin kasar kacokan, inda sauran dimbin al’umma kuma ke ci gaba da shan matukar wahala. Amma har yanzu mun kasa gane wadannan tsirarun mutane, wadanda ke amfanuwa da tallafin man fetir iya su kadai, ko su wane ne wadannan mutane, oho. Yanzu bayan cire wannan tallafi da aka yi, wane shiri ko tanadi kuma aka yi, wanda zai rage wa al’umma wannan radadi, tun yanzu ta kai ga wasu ba ma sa iya amfani da ababen hawansu, sakamakon tsadar da man ya yi.
Babban abin da ya rage mana yanzu shi ne, yin nazari kan yadda za mu fara tace namu man a nan cikin gida Nijeriya. Idan muka fara tace man, zai yi matukar sauki ta yadda za mu amfani da shi a nan, abin kuma da ya rage mu fitar da shi kasashen waje mu sayar.
Wace shawara za ka ba wa ‘Yan Nijeriya, musamman al’ummar Nupe?
Muna yi wa godiya da ya nuna mana wannan lokaci. Sannan, muna gode wa sauran al’umma wadanda ke taimaka mana tare da ba mu gudunmawa daga bangare daban-daban. Musamman wadanda ke amsa kiranmu a duk lokacin muka nemi wani tallafi nasu wanda zai taimakawa ci gaban al’umma cikin gaggawa. Muna sake yi musu godiya ta musamman tare da fatan Allah ya saka musu da mafificin alhairi, ya kuma biya musu dukkanin nasu bukatun. Muna kuma addu’ar Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya mai dorewa a wannan kasa tamu mai albarka Nijeriya. Sannan, muna kara addu’a Allah ya canja mana zukatan dukkanin wadanda ke amfani da wata dama tasu wajen kisan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba tare da lalata musu dukiyoyinsu. Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya a wannan kasa tamu mai albarka, amin.