Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home FASIHAI

Tattaunawa Ta Musamman Da Marubucin Littafin ‘Zuciyarka Jagorarka’, Mustapha Abdullahi

by Sulaiman Ibrahim
February 11, 2021
in FASIHAI
4 min read
‘Zuciyarka Jagorarka’
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake kasancewa daku a filin ku na FASIHAI. Shafi  da ke zakulo muku shahararrun marubuta da mawakan hausa, tare da wakiliyar LEADERSHIP A YAU, SADIYA SIDI SAID, wacce aka fi sani da SIDIYA.

A wannan makon muna tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI, daya  daga cikin marubutanku. Ya nishadantar da ku a cikin littafai da dama, inda kuma shine ya rubuta fitaccen littafin nan mai cike da dimbin ilimi da hikima mai suna ‘Zuciyarka Jagorarka’. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

samndaads

 

Malam Mustapha, masu karatu za su so jin dan takaitaccen tarihinka?

 

Ya aka yi ka tsinci kanka a harkar rubuce-rubuce?

Saboda ina yawan karance karance, kwatsam sai na tsinci kaina ina rubutu

 

Tsawon wani lokaci ka dauka a harkar rubutu, sannan daga fara rubutunka zuwa yanzu littafi nawa ka rubuta?

Shekara biyar kenan zuwa shidda. Na rubuta littafi guda biyar, na buga biyu

 

  1. Zuciyarka Jagorarka 1, 2.Open The Page, 3. Zuciyarka Jagorarka 2, 4. Lafiya Uwar Jiki sai na 5. Kuotes for Thought

 

Daga cikin jerin gwanen littafanka wanne ne bakandamiyarka, ma’ana wanda ka fi so ka kuma fi jin dadi yayin rubuta shi? Sannan kuma wanne yafi ba ka wahala wurin rubutun shi?

Bakandamiyata shi ne Zuciyarka Jagorarka.  Wanda yafi ban wahala kuwa Open the page

 

A dunkule wasu sakonni wa’yannan littafai guda biyu ke dauke da shi?

Na Hausa su na karawa masu karatu illlmi ne game da yadda jikinsu yake. Na turancin kuma su na zaburar da masu karatu wajen zage damtse wajen neman ilimi

 

Malam Mustapha na da aure ko kuma sai dai niyyar yi?

Ba ni da aure, sai dai niyya.

 

A ganin ka rubutu dace ne da cancanta ko kuwa kowa ma ze iya zama marubuci/marubuciya?

 

Me Malam Mustapha yafi so ta bangaren, abun sha da kuma nau’in sutura?

Ina son kankana sosai. Sutura kuma ina son kufta

 

Eh kwarai kuwa zamani ya zo da dole marubuta su fadada tunaninsu, su rungumi yada rubutunsu a yanar gizo.  Tabbas akwai dubban mutane masu karanta rubutunmu. Kenan mutum zai iya siyar da rubutun sa a wannan kafa

 

A iya wallafa littafai wasu da yawa su ka san malam Mustapha. Kasancewar muna wani karni dake tafiya da zamani, kai ba ka rubuta labaran wasan kwaikwayo ne ko masu dogon zango?

Eh to, ba na rubutun wasan kwaikwayo, haka ma na mai dogon zango, amma ina tunani akai

 

Wani shawara za ka bai wa masu karatu har ma da marubuta ‘yan uwanka?

Marubuta hadin kai,  zurfin tunani, da hikima, sai kuma dagewa wajen neman gogewa da kwarewa a fagen rubutun. Makaranta kuma yin uzuri ga marubuta,  babsu shawara,  nuna musu batutuwan da su ka dace ayi rubutu a kansu

 

Su waye taurarinka cikin marubuta mawallafa da ma na yanar gizo, wanda rayuwar shi/ta ke burge ka?

Ado Ahmad Gidan Dabino,  Tijjani Muhammad Musa,  Fauziyya D Sulaiman,  Adamu Yusuf Indabo,  Khalid Imam,  Badamasi Aliyu, Bello Sagir da sauransu.

 

Wani sako ka ke dauke da shi zuwa ga masoyanka, sannan kamar ga masu neman littafanka, ta wace hanya za su iya samu a saukake, akwai wa’yanda ka sake a yanar gizo ne ko kuma se dai a kasuwa?

Ina yi wa masoyana fatan alkhairi da kuma nuna godiya ga addu’an da su ke yi min. Allah ya bar zumunci.  Game da litattafaina,  na saki Zuciyarka Jagorarka da open the  page a okadabooks na yanar gizo. Haka kuma ana samun littafin Zuciyarka Jagorarka a kasuwa da supermarkets na Kano.  Na turanci kuwa ina sa rai zai shiga kasuwa a wannan shekara insha Allah

 

Mene ne burinka nan gaba kadan game da rubutunka?

Burina shi ne rubutuna ya shiga duk wani lungu da sako inda ake yin hausa domin jama’a su ilimintu, su san yadda jiki yake da yadda za su inganta lafiyar su, da kuma kara tunatar da su muhimmancin karatu da neman ilimi

 

Malam Mustapha, LEADERSHIP A YAU na yi maka fatar alkhairi.

Nagode kwarai. Masha Allah.

SendShareTweetShare
Previous Post

Manoman Alkama Na Fuskantar Matsalar Samun Kayan Aiki

Next Post

Mun Kuduri Aniyar Yashe Magudanan Ruwa Don Magance Zaizayar Kasa – Shugaban NEWMAP, Usman Ibeto

RelatedPosts

Na Tsinci Kaina A Waka Ne Kasancewar Mun Rayu Da Sha’iri Auwal – Jakadan Fadima

Na Tsinci Kaina A Waka Ne Kasancewar Mun Rayu Da Sha’iri Auwal – Jakadan Fadima

by Sulaiman Ibrahim
1 month ago
0

Assalamu Alaikum. Barkan mu da sake kasancewa daku a filin...

Fim

Da Farko Ba Na Sha’awar Harkar Fim –Jaruma Amina Sharada

by Muhammad
1 month ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Masana’anta shirya fina-finan Hausa (Kannywood) kasancewar...

Sharifiya

Kafin Na Tsinci Kaina A Harkar Waka Sai Da Na Fara Rubutu –Mai Sharifiya

by Muhammad
2 months ago
0

Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake kasancewa da ku a filinku...

Next Post
Usman Ibeto

Mun Kuduri Aniyar Yashe Magudanan Ruwa Don Magance Zaizayar Kasa – Shugaban NEWMAP, Usman Ibeto

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version