Da yammacin jiya Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ta wayar tarho, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan huldar da ke tsakanin kasashen 2, da kuma batun rikicin Ukraine.
Har ila yau a dai wannan rana, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin Turai da Asiya, na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Yu Jun, ya yi wa kafofin yada labaru na gida da wajen kasar Sin bayani, inda ya ce zantawar shugabannin 2, ta nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da tsayawa kan matsayinta don gane da batun Ukraine, kuma tana sauke nauyi dake wuyanta, game da al’amuran kasa da kasa bisa adalci da sanin ya kamata.
Yu ya kara da cewa, bayan da rikicin Ukraine ya yi kamari, shugaba Xi Jinping ya gabatar da ra’ayoyinsa domin daidaita rikicin, kana kasar Sin ta kaddamar da takardar matsayin ta game da daidaita rikicin Ukraine a siyasance, inda ta gabatar da ka’idoji 12. Alal misali, akwai bukatar girmama ikon mulkin kasa, da yin watsi da tunanin yakin cacar baki, da tsagaita bude wuta, da dasa aya ga yake-yake, da fara gudanar da shawarwarin zaman lafiya.
Ban da haka kuma, kasar Sin ta sa kulawa sosai kan halin jin kai a Ukraine, ta kuma gabatar da ra’ayinta kan sassauta zaman dardar a kasar, tare da bai wa Ukraine taimako gwargwadon karfinta.
Jami’in ya ce har kullum kasar Sin na goyon bayan matakan shimfida zaman lafiya, tana kuma son hada kai da kasashen duniya, wajen ci gaba da taka rawarta mai yakini, a fannin daidaita rikicin na Ukraine a siyasance. (Tasallah Yuan)