Daga Abdullah Muhammad Sheka,
A ranar lahadi ne tawagar Gwamnatin Jihar Kano karkashin mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna suka kaiwa Tsohon Gwamnan Jihar Kano Injinya Rabiu Musa somin Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifinsa a gidansa dake Kano. Kamar yadda Daraktan yada labaran Mataimakin Gwamnan Hassan Musa Fagge Shaidawa LEADERSHIP A Yau. Za’a
Tawagar wadda keyin karkashin Jagorancin mataimakin Gwamnan Jihar Kano, kwamishinoni, mashawarta na musamman da mayan shugabannin sassan ma’aikatun Gwamnatu.
Da ya ke gabatar da sakon Ta’aziyyar Dakta Gawuna ya ce, “na so a ce Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje nee ya Jagoranci zuwa wannan Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Tsohon Gwamnan, Makama. Karaye Alhaji Musa Saleh Kwankwaso.
“Mu na addu’ar fatan Allah ya bashi aljanna madaukaciya, ya Kuma bamu ikon jure Wannan babban Rashi wanna mutumin kirki,” in ji Gawuna.
Da ya ke karbar gaisuwar tawagar ta Gwamnatin Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwasiyys ya godewa mataimakin Gwamnan bisa wannan ziyara.
Hakazalika tawagar ta ziyarci gidan Kadiriyya Wanda ya rigamu gidan gaskiya bayan fama dayajeruwar rashin lafiya.
Mataimakin Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikansa ya kyautata makwancinsu.