An tsara cewa, jakadun da suka hada da na kasashen Madagascar da Bahrain da Nepal da Bahamas da Slovakia da sauransu, za su ziyarci Lanzhou, babban birnin lardin Gansu, da Dunhuang da ya kasance muhimmin wurin yada zango a kan hanyar siliki da sauran biranen lardin.
Bayan isarsu Lanzhou a jiya Laraba, jakadun sun ziyarci kamfanin hada magunguna na Foci da kamfanin Lanzhou LS Group, katafaren kamfanin kera kayayyakin sarrafa albarkatun man fetur.
- Samun Bunkasuwa Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
- Kasar Sin Na Hada Kai Da Kasa Da Kasa A Kokarin Inganta Muhallin Halittun Duniya
A kamfanin Foci, jakadun sun nuna matukar shaawarsu ga dadadden tarihin kamfanin na hada magunguna da kuma tarin magungunan gargajiya da yake sarrafawa.
Da yake jawabi, babban jamiin ofishin jakadancin Nijeriya a kasar Sin, Babagana Wakil, ya ce suna koyo da ganin tarin sabbin abubuwa. Yana mai ganin cewa, abu ne mai muhimmanci rungumar maganin gargajiya na kasar Sin, saboda yadda yake da inganci da kuma amfani. (Mai fassara: Faiza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp