Tawagar ‘yan sama jannati na Shenzhou-14, sun shiga kumbon dakon kaya na Tianzhou-5, a yau Lahadi.
‘Yan sama jannatin sun bude kofar kumbun Tianzhou-5 ne da misalin karfe 2 na rana agogon Beijing, inda suka shiga ciki da misalin karfe 3:03 na yamma, bayan sun kammala shirye-shirye.
Tawagar ta Shenzhou-14, za su yi aikin kwashe kayayyaki da sauran wasu ayyuka a cikin kumbon.
Kasar Sin ta tura kumbon Tianzhou-5 ne a jiya Asabar, domin kai kayayyaki zuwa tashar binciken sararin samaniya ta kasar, wanda ake sa ran kammala ginisa a bana. (Fa’iza Mustapha)