Dunƙulen magi na Terra ya yi fice a tsakanin kamfanoni takwarorinsa masu haɗa sinadarin ɗanɗanon girki a Nijeriya, saboda inganci da ɗanɗanonsa na musamman ne da ya wuce sauran, inda ake iya amfani da shi a girke-girke iri-iri daban-daban.
A cikin shekarun da suka gabata, Terra ya samu wurin zama babba a masana’antar ɗanɗanon kayan girki, ya zama mashahuri a wurin masu dafa abinci a faɗin Nijeriya da ƙetare.
- Gwarzon Kamfani A Shekarar 2024: AVSATEL Communications Limited
- Gwarzon Wasannin Motsa Jiki Na Shekarar 2024: Bambo Akani
Sinadaren da ke cikin dunƙulen Terra, su ne sirrin dandanon shi, don yana bayar da wani sirrin ɗanɗano na musamman ga kowa da kowa. Dunƙulen yana zuwa ne a ɗanɗano kala uku: Mai ɗanɗanon naman shanu da kaza da shinkafa dafa duka.
An samar da kowanne ɗanɗano daga cikin ukun da aka lissafa, don komai ya tafi tare da inganta asalin ɗanɗanon abincin gargajiya, yana taimaka wa masu dafa abincin gargajiya da na zamani wajen sarrafa abinci mai ban sha’awa.
Dunƙulen magin Terra, babban sinadari ne na girke-girke da yawa, wanda za a iya amfani da shi wurin dafa abincin gargajiya.
Sinadaren shi, sun bayar da damar yin amfani da Dunkulen Terra wajen sarrafa abincin gargajiya na Nijeriya kamar miyar egusi da miyar kuka da miyar tumatir da shinkafa dafa duka da kuma girke-girke na zamani.
Baya ga haka, Dunƙulen magin Terra sun dace da sauran girke-girke kamar farfesun kaza da kifi da naman shanu.
Dunƙulen magin Terra an samar da shi ne ta hanyar haɗe-haɗen sinadarai na asali don tabbatar da cewa, dunƙulen ba shi da cutarwa ga lafiya, sai dai samar da ɗanɗano da abinci mai gina jiki.
Wannan fice da yabo da Terra ke samu, ba a baki kaɗai ko a rubuce ya ke ba. A cikin shekara 2022, an karrama kamfanin dunƙulen Terra da Kyautar Mafi kyawun Dunƙulen sinadarin girki na shekara. Wannan lambar yabo ta tabbatar da jajircewa da sadaukarwar kamafanin na samar da kayayyaki masu inganci wadanda suka dace da buƙatun abokan ciniki.
Lambar yabon ta kuma nuna sadaukarwar Terra na ci gaba da haɓakawa da kiyaye matsayinsa a matsayin amintaccen kamfani a tsakanin masana’antar kayan ɗanɗanon girke-girke.
Lambar yabo da Tare ya samu saboda sadaukarwa da samar da dandano mai inganci ga abokin ciniki.
Dunƙulen Magin Terra, ya cancanta ya zama Gwarzon Kamfanin Dunkulen magi na kamfanin LEADERSHIP a shekarar 2024.