Muh'd Shafi'u Saleh" />

TETFUND Ta Mika Kyautar Injinan Dab’i Ga Jami’ar Modibbo Adama

A wani shirin inganta fannin dab’i, hukumar tallafawa manyan makarantu (TETFUND), ta mika injinunan dab’i na zamani ga jami’ar Modibbo Adama dake Yola.

Injunan wanda kamfanin TEKRA Global Concepts ya samar sun hada da; Konica Minolta Accurio Printing Machine, Champion Digi-band binding Machines, Champion Digi-Cut Cutting Machine, Champion Stitching da Champion Laminating Machine, za’ai aikin buga littattafai, mujalku, da ake jin zai kawo saukin aiki ga malamai da dalibai.
Haka kuma cibiyar zata rage yawan dogaro da kamfanonin waje, wajan dab’i da karfafa shehunan jami’ar da kuma harkar wallafa a manyan makarantun kasarnan.
A yayin da yake bayani kan cibiyar mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Abdullahi Liman Tukur, wanda ya bayyana nasarorin da samar da injunan zai cimma, ya ce zasu kuma kara yawan kudaden shigar da jami’ar ke samu.
Ya ce “wannan cibiyar ta na iya samarwa da buga littatafai masu yawa a rana guda” inji Farfesa Liman.
Da shi ma ya ke tasa maganar, dan kwangilar Mista Franklin Ogbuagu, ya ce cibiyar za ta iya samar da kimanin Naira miliyan 50 zuwa 100 a wani wata idan sun fara aiki yadda ya kamata.
An dai yi yarjeneniya tsakanin dan kwangilar injunan da jami’ar kan zai horar da ma’aikatan jami’ar 10 yadda za su ci gaba da kula da injinan.

Exit mobile version