A karon farko a cikin shekaru kusan 30, babbar jam’iyyar siyasa a Nijeriya ta zabi ‘yan takararta na zaben shugaban kasa dukkkansu Musulmai.
Wannan mataki da jam’iyyar ta dauka ya jawo ce-ce-ku-ce a bangarori da dama a Nijeriya, tun daga bangaren musulmi zuwa wadanda ba musulmi ba.
Mataki da jam’iyyar APC ta dauka bai ci karo da kundin tsarin mulkin Nijeriya ba, hasali ma duk nazari da bincken masu bincike ba su iya kawo wata matsala a kan haka ba daga tsarin mulki da kuma tarihi, kusan ma za a iya cewa tarihi ne ya maimaita kansa don an taba yin shugaba da mataimakinsa a mabiya addini daya a madafun iko ba sau daya ba, ba sau biyu ba.
A zamanin mulkin soja, Janar Johnson Aguiyi Ironsi da Babafemi Ogundipe dukkansu kiristoci ne da suka mulki Nijeriya, babu abin da ya faru har suka kammala mulkinsu.
A tsakanin shekarun 1966-1975, Janar Yakubu Gowon da Joseph Akinwale sun yi mulki a Nijeriya zamanin mulkin soja kuma dukkansu mabiya addinin kirista ne, kuma sun yi lafiya lau babu abin da ya faru.
A shekarar 1978, Cif Awolowo Obafemi ya dauki Kirista a matsayin abokin takararsa duk da cewa shi Kirista ne, wato Cif Umeadi Phil daga Jihar Anambra, shi ma wani misali ne kan hade ‘yan takara mabiya addini daya.
Haka kuma shugaban kasar Nijeriya na farko bayan samun ‘yancin kai, Dakta Nnamdi Azikwe, a shekarar 1979 ya yi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NPP, wanda ya dauko Farfesa Ishaya Audu daga Jihar Kaduna a matsayin mataimakinsa, inda shi Ishaya kirista ne.
A shekarar 1993, Masud Abiola (MKO) tare da Baba Gana Kingibe sun yi takara a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa su ma matsayin musulmi da musulmi, Abiola daga yankin Yarbawa, sai Baba Gana daga Jihar Borno.
Shugaban sashen shari’a na kwamitin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu a 2023, Babatunde Ogala SAN, ya ce Tinubu bai saba wata doka ba don ya zabi musulmi ya zama abokin takararsa duk da shi yana musulmin.
Ogala ya kare maigidansa a game da daukar musulmi da ya yi, ya jawo tikitin Musulmi da Musulmi. Ya kuma yi karin haske a kan abin da tsarin mulki ya tanada.
Ya ce, “Abin da za a duba da farko shi ne, shin Tinubu ya yi wani abin da ya saba wa doka wajen daukar abokin takara? Dole mu koma wa sashe na 14 da 15 na dokar kasa.
“Dokar ta yi maganar adalci da gaskiya wajen rabon dukiyar kasa, amma ba ta kawo batun addini ba. Dokar ta yi bayanin bambance-bambance da wakilcin al’umma. Tsarin mulki bai yi batun addini ba, saboda haka ba zai yiwu a ce an ware wasu ba.”
Sai dai kuma, Kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) ta ce ba za ta mara wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC baya ba, don ya zabi musulmi a matsayin abokin takararsa.
Shi ma da yake bayyana ra’ayinsa, wani malamin addinin Musulunci a Kaduna, Sheikh Halliru Abdullahi Maraya ya ce hada mabiya addini daya su kasance shugaban kasa da mataimaki a kasa mai al’ummar musulmai da kirista ya saba wa ka’idar addinin Musulunci.
Shehin malamin wanda tsohon mai bai wa gwamnan Jihar Kaduna shawara ne kan harkokin addinin Musulunci, ya ce adalci shi ne ya fi dacewa wajen gudanar da mulkin kasa. Malamin ya ce a mulki gaba daya ba abin da ke sa a samu a nasara illa a yi adalci.
Ya ce, “Shi Musulunci addini ne da yake so a ko da yaushe a yi wa wadanda ba sa yinsa adalci kuma a kyautata musu, ma’ana a ba wa kowanne mai hakki hakkinsa.”
Ya kuma kara da cewa a mataki na iko, addinin Musulunci ya tanadi cewa a yi wa kowa adalci, ka da kiyayya ta mutane ta sa a daina yin adalci, don haka ya kamata a yi mulki ta yadda za a tafi da kowa. Ya bayar da misali da Jihar Kaduna da yanzu musulmi da musulmi ne ke jagoranci, ya ce me al’ummar musulmi suka amfana da mulkin?
Ita ma jam’iyyar APC a matakin kasa ta kare matsayinta na cewa Kiristocin Nijeriya su kwantar da hankalinsu babu abun da zai faru don jam’iyyar da dauki matakin bai wa musulmi da musulmi takaran shugabancin kasa da mataimaki, domin ta duba dacewa ne ba addini ba.
Koma dai mene ne abubuwan da al’umma za su rika la’akari da su shi ne, ingancin ‘yan takara da amfaninsu ga ci gaban kasa ba addini ko kabila ko bangaren da ‘yan takara suka fito ba.
…Kalubalen Da APC Ke Fuskanta Bayan Shan Kaye A Osun
A karshen makon da ya gabata ne aka gudanar da zaben Gwamna Jihar Osun, inda babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta lashe zaben gwamna. Masu nazarin siyasa a Nijeriya na ganin wannan shan kayen da jam’iyyar APC ta yi ba karamin kalubale ba ne a gare ta yayin da take fuskantar babban zabe na 2023, domin Jumma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta.
Idan aka yi waiwaye a baya-bayan nan, a shekarar 2014, jam’iyyar PDP da ke kan mulki, ta fada wani rikicin cikin gida wanda daga bisani ya zama daya daga cikin dalilan da suka sanya jam’iyyar ta rasa mulki a zaben 2015.
Irin wannan ma ya kunno kai a cikin jam’iyyar ta APC, wanda ‘ya’yan jam’iyyar suke ficewa daga jam’iyyar suna shiga wasu jam’iyyun mabambanta.
Shi kansa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce kayen da jam’iyyar ta sha a zaben gwamnan Jihar Osun jarrabawa ce daga Allah.
Ya kara da cewa ya zama wajibi ga ‘ya’yan jam’iyyar su gyara abubuwan da suke yi wadanda ba daidai ba ne game da tafiyar da lamuran siyasar Nijeriya gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
Haka kuma Adamu ya tabbatar da cewa barakar da ke tsakanin manyan ‘ya’yan jam’iyyar ne ya haifar da faduwar ta a zaben na Osun.
Ya kara da cewa wadannan jiga-jigai na jam’iyyar APC a Jihar Osun sun rika suka da zargin junansu har wasu na cewa ba za su yi zabe ba, don ba a yi masu abun da suke so ba. Ya tabbatar da cewa jiga-jigan na APC a jihar sun kasa jituwa a tsakaninsu duk da cewa suna a jam’iyya daya.
Wasu kuma na ganin giyar mulki ce ta ja wa jam’iyyar APC faduwa zaben gwamnan Jihar Osun, inda Gwamna Oyetola ke taka duk wanda ya so a jihar ba tare da la’akari da iyayen gidansa ba, ciki kuwa har da tsohon maigidansa kuma tsohon Gwamnan jihar kuma Minista a yanzu wato Rauf Aregbsola, wanda Oyetola ya yi shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar lokacin yana gwamna.
Ire-iren wadannan abubuwa da suka faru a jam’iyyar APC a Jihar Osun zai iya samun ta a matakin kasa don kuwa akwai wadanda aka bata wa da yawan gaske a cikin jam’iyyar, wadanda ake ganin za su iya kawo wa jam’iyyar matsala a babban zaben shekara ta 2023, musamman ma ‘yan majalisu da ba za su koma kujerunsu ba.
Wata majiya ma ta ambato gwamnoni jam’iyyar APC musamman wadanda suke yankin arewa maso yamma suna kullace da uwar jam’iyyar APC ganin cewa ba a bai wa daya daga cikinsu takarar mataimakin shugaban kasa ba.
Wakazalika, wani kalubale da ake ganin jam’iyyar na fuskanta shi ne bangaren Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru el-Rufai ana kishin-kishin ya fara takun saka a tsakaninsa da takarar jam’iyyar saboda rashin ba gwamnan matsayin mataimaki. Sai dai babu wata sanarwa baro-baro a fili kan wannan, amma rashin halartarsa taron kaddamar da Shettima a matsayin mataimaki ya nuna ruwa ba ya tsami banza.
Ana ganin cewa shugabannin APC ne suke boye rikicin a tsakaninsu domin kar a masu dariya kamar yadda ta kiceme a PDP tsakanin Atiku da Wike.
Biyo bayan kayen da jam’iyyar ta sha a zaben Osun, wasu shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar APC a arewa ta tsakiya sun yi kira ga shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Abdullahi Adamu da ya yi murabus.
Wata kungiya kuma ta ce tuni shugaban jam’iyyar na kasa ya gaza kuma idan ya ci gaba da kasancewa a matsayin shugaban jam’iyyar za su yi babban rashi a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban kungiyar, Saleh Mandung Zazzaga, a madadin ‘ya’yan kungiyar ya yi wannan kiran a Jos, babban birnin Jihar Filato a wata hira da ya yi da manema labarai.
“Adamu kafin zaben (na Osun) ya sha alwashin kawo wa jam’iyyar Osun, amma yanzu ya kasa cikawa, wanda ya janyo babbar jam’iyyar adawa tana samun karin karfi.”
A cewarsa, “Halin girman kan shugaban jam’iyyar da rashin hakuri da shawarwari ya sanya ‘ya’yan jam’iyyarmu da dama suka yi watsi da jam’iyyar, su ma sun fara debe tsammani a jam’iyyar.
“Muna so mu yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su bukaci shugaban jam’iyyar na kasa da ya yi murabus ko kuma a kira shi a ba shi tsarin da ya dace, sannan kuma a dora masa alhakin gudanar da ayyukansa, domin ka da jam’iyyar ta sha kaye a 2023, domin zaben zai yi zafi tun daga kasa zuwa sama a matakan jihohi da kananan hukumomi ciki har da na bangaren ‘yan majalisa.
Ya yi kira da a gaggauta kafa kwamitin sulhu na kundin tsarin mulki domin kwantar da hankulan ‘ya’yan jam’iyyar daga faduwa zaben fid da gwani a fadin jihohi da kuma tarayya, domin su ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar da kuma yin aiki wajen samun nasara.
Ko da yake a kokarin da shugaban jam’iyyar APC na kasa yake yi wajen kare kansa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi kira da ‘ya’yan jam’iyyar su kwantar da hankalinsu, kuma su rungumi kaddara a kan wannan faduwar zaben da aka yi.
A cewarsa, jam’iyyar za ta duba abubuwan da suka janyo ta fadi zaben Osun, domin gyara saboda samun nasara a zaben kasa mai zuwa.
“Harkar siyasa kamar sauran harkokin rayuwa ne, wata rana ka samu, wata rana kuma ka rasa. Iko ne na Allah, babu yadda muka iya dole mu dauki kaddara.”
Abdullahi Adamu ya ce ba an kayar da APC ba ne saboda rashin iya siyasa, sai dai matsalolin da ke tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar gabanin zaben.
Koma dai mene ne ya kamata jam’iyyar APC ta dauki matakan gyara tun kafin lokaci ya kure mata, ka da ta yi abun nan a ake cewa ‘fargar jeji’ wanda ba zai yi amfani ba.
Wasu Manyan Dalilan Da Suka Sa APC Ta Rasa Osun
Bincike ya nuna cewa jam’iyyar APC ta yi rashin nasara a zaben gwamna a Jihar Osun daga hannun babbar jam’iyyar adawa ta PDP da kuri’u 28,353, sakamakon rashin sulhunta ‘yan takarar da suka tsaya zaben fid da gwani a karkashin jam’iyyar tun daga matsayin gwamna da majalisar dattawa da na wakilai da kuma majalisar dokokin jiha.
Lallai rikicin cikin gida ya yi babban tasiri wajen janyo faduwar jam’iyyar APC da kuma hana Gwamna Adegboyega Oyetola ci gaba da yin mulki karo na biyu a Jihar Osun.
Binciken LEADERSHIP ya bayyana cewa rashin sulhunta shugabannin jam’iyyar APC, musamman Gwamna Oyetola da ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya yi babban tasiri wajen rashin nasarar jam’iyyar a jihar.
Rikicin shugabannin jam’iyyar a tsakanin wadannan jiga-jigan ‘yan siyasan ta fara kunno kai ne tun bayan kammala zaben shugabannin jam’iyyar a jihar a shekarar 2021, tun daga na gundumomi da na kananan hukumomi da na jihar, wanda ya haddasa rarrabuwar kai tare da rashin jituwa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar, musamman ma magoya bayan bangarorin guda biyu.
Haka kuma rikicin ya yi tasiri wajen gudanar da zaben fid da gwani, domin dukkan su sun nuna karfin ikosu, amma dai daga baya Oyetola ya samu nasarar lashe zaben fid da gwani.
An dai dauki tsawan lokaci wajen kokarin sasanta wadannan jiga-jigan jam’iyyar guda biyu kafin gudanar da zaben gwamnan, amma hakan ya ci tura.
Idan za a iya tunawa ma Aregbesola ya ki halartar ganganmin yakin neman zabe na jam’iyyar ballantana har ya bayar da gudunmuwa a zaben.
Sauran dalilan da ya sa jam’iyyar APC ta fadi zaben dai sun hada da kin tattara kudade ga shugabannin jam’iyyar saboda zaben, sannan kudin da Oyetola ya fitar ba su taka kara sun karya ba, wanda hakan ya janyo babban jam’iyyar adawa ta PDP ta samu nasarar lashe zaben.
Haka kuma wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC sun koma PDP sakamakon muzgunawa daga shugabannin APC, wanda hakan ya kara yawan kuri’un da jam’iyyar adawan ta samu.
Bincike ya tabbatar da cewa Oyetola na takarar jam’iyyar APC ya fadi zaben gwamnan Jihar Osun da ya gudana a ranar 16 ga watan Yuli ne sakamakon jam’iyyar ta kasa magance rikicin cikin gida a tsakanin ‘ya’yanta, musamman rabuwar kan da ke tsakanin gwamnan da Aregbesola, wanda aka ganin ya taimaka wa PDP wajen lashe zabe.
Alal misali, tsohon kwamishinan kananan hukumomin Jihar Osun da harkokin sarauta, Kolapo Alimi ya koma jam’iyyar PDP ana saura kwana biyar da gwamanar da zaben. Inda nan take aka nada Alimi a matsayin darakta janar na yakin neman zaben Sanata Ademola Adeleke, saboda karfin da yake da shi.
Alimi ya rike mukamin kwamishinan jihar lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Rauf Aregbesola a wa’adin mulkinsa na biyu.
Bincike ya tabbatar da cewa magoya bayan ministan harkokin cikin gida sun daka muhimmiyar rawa wajen kayar da gwamnan Jihar Osun daga kan karagar mulki, wanda ya sa jam’iyyar APC ta rasa kujerar gwamna a jihar.