Wani dan gwagwarmayar siyasa kuma tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Kwamared Timi Frank, a ranar Litinin ya yi kira ga shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, da ya yi bayani kan zaben da ya gabata cikin gaggawa, ya yi murabus daga mukaminsa ko kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya yi abin da ake bukata ta hanyar sauke shi daga mukaminsa.
Acewar Frank, bai taba ganin zabe mafi muni da aka taba yi a tarihin Nijeriya ba sama da wanda aka gudanar a 25 ga watan Fabrairun, 2023.
Ya yi kira ga shugaba Buhari da ya jajirce wajen sauke Farfesa Yakubu sabida ya jawo wa kasar nan abin kunya ta hanyar bayyana sakamakon da bai dace ba wanda ke cike da magudi a dukkan zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka kammala.
Frank, wanda ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa a Abuja a ranar Litinin, ya ce lokaci ya yi da shugaban hukumar INEC ya dace ya yi murabus sabida ‘yan Nijeriya sun rasa kwarin guiwar amincewa da shi.