Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya ce Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ba ya tsoma baki ko katsalandan a ayyukan hukumar.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today, Olukoyede, ya ce wasu na ƙoƙarin ɓata wa Shugaban Ƙasa suna, suna zarginsa da amfani da EFCC don muzgunawa ‘yan adawa.
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Aiki Kan Rigakafin Covid -19
- Kwastam Ta Kama Jirage Marasa Matuka Da Sauran Kayayyaki Da Darajarsu Ta Haura Naira Biliyan 921 A Legas
Ya ce waɗanda ke kusa da Tinubu za su iya shaida cewa burinsa kawai shi ne ganin gwamnati ta yi aiki yadda ya kamata, ba wai amfani da hukumomi don biyan buƙatunsa na siyasa ba.
Olukoyede, ya ƙara da cewa EFCC ta kama da dama daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki fiye da yadda ta kama na jam’iyyun hamayya, alamar cewa hukumar ba ta nuna bambanci ba.
An daɗe ana zargin cewa hukumomi irin EFCC na zama karen farautar gwamnati wajen danniya ko hukunta ‘yan adawa.
Amma shugaban EFCC ya ce hakan ba gaskiya ba ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp