Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana cewa; ko kaɗan gwamnatin Tinubu ba ta shirya gudanar da sahihin zaɓe a 2027 ba.
Galadima ya bayyana haka ne, a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise.
Ya ce, “Wannan gwamanatin, ko kaɗan ba ta shirya gudanar da sahihin zaɓe ba, kamar yadda suke ɓata jam’iyyu; hakan ne yake nuna cewa, ba sa ƙaunar adawa ko kaɗan, musamman idan lokacin zaɓe ya zo”.
- Tinubu Ya Halarci Ɗaurin Auren Ɗan Yari, Ya Kai Ziyara Gidan Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari.
- Tinubu Ya Ci Amanar Kano, Babu Batun Haɗin Guiwa Tsakaninsa Da Kwankwaso A 2027 – Galadima
A cewar Galadima ana raɗe-raɗin cewa, shugaban ƙasar na shirin naɗa wani ɗan kama-karya a matsayin shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa.
Galadima ya yi matuƙar gargaɗi ga wannan tare da cewa; yin hakan zai iya dagula zaman lafiyar ƙasar ko kuma haifar da wani yaƙin na Basasa.
Ya ƙara da cewa, “Ina fatan hakan ba gaskiya ba ne, domin kuwa idan wannan mutum ya zama shugaban INEC, ko shakka babu; wannan gwamnati kai tsaye na gayyato yaƙin Basasa ne.”
Da yake mayar da martani a kan batutuwan da jam’iyyun siyasa suka fara yi na yaƙin neman zaɓe, ya zargi hukumar zaɓe ta ƙasa da gazawa waje aiwatar da dokokin yaƙin neman zaɓe.
“Wannan batu na yaƙin neman zaɓe kafin hukumar INEC ta ba shi dama, gwamnatin wancan lokacin ce ta fara yin hakan, wanda kuma hakan ke nuni da cewa; hukumar INEC ba za ta iya yin alƙalanci na gaskiya da adalci ba,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa; jam’iyyun adawa sun “Faɗa tarkon” APC ta hanyar shiga yaƙin neman zaɓe da wuri.
Har ila yau, a zaɓen cike gurbi na baya-bayan nan, Galadima ya yi watsi da nasarar da APC ta samu, inda ya yi misali da Jihar Kano da Zamfara, musamman ganin yadda jami’an tsaro suka tsorata masu kaɗa kuri’u”.
Ya ƙara da cewa, “Ba su ci zaɓe ko guda ɗaya ba, amma sun sanar a matsayin su ne waɗanda suka lashe zaɓen. A mazaɓar Bagwai da Shanono, mun samu ƙuri’a 16,000; yayin da APC ta samu ƙuri’a 5,000. A wata ƙaramar hukumar kuma, NNPP ta samu sama da ƙuri’a 5,700, yayin da APC kuma ta samu ƙuri’a 265 kacal.
“Sama da sojoji 30,000 aka kai Zamfara, domin aiwatar da zaɓukan mazaɓu biyar kacal. An yi wa mutane dukan tsiya, an nakasa wasu, an kori wasu, sannan a ƙarshe sun rubuta wa kansu sakamakon zaɓen tare kuma da bayyanawa.”
Dangane da irin ƙarfin da jam’iyyar NNPP ke da shi, Galadima ya bayyana cewa; Shugabanta Rabiu Musa Kwankwaso, ba shi da abokin karawa idan ana batu na tasiri a siyasance.
“Kwankwaso shi ne babban jigon siyasar Nijeriya, domin kuwa shi kaɗai ne, wanda tauraronsa yake haskawa; saboda haka, idan har za a yi zaɓe na gaskiya, shi ne mafi farin jini a Nijeriya,” in ji shi.
Haka zalika, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa; Kwankwaso ya gana da shugaba Bola Tinubu kwanan nan.
“Ƙarya ne batun cewa, Kwankwaso ya gana da Tinubu a Faris. Ai wannan cin fuska ne ma, ta yaya za ka yi wa wanda ya ayyana ka a matsayin maƙiyi aiki?” Ya ƙara da cewa, NNPP ta kori waɗanda suka yi iri wannan ta’asa ba tare da amincewar jam’iyyar ba.
Dangane da ƙawancen siyasa kuma, Galadima ya ce; son kai a tsakanin ƴ an adawa, shi ne musabbabin hana haɗin kai a tsakaninsu.
“Zan so dukkaninmu mu haɗu mu ceci wannan ƙasa tamu baki-ɗaya, amma dukkaninmu, mun san wa da wa ya kamata a tsayar a Nijeriya, domin samun nasarar lashe zaɓe?
Ya kuma nuna farin cikinsa da batun tattaunawar da aka samu rahoto cewa, ana yi tsakanin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour Party, inda ya bayyana cewa, “Idan za su iya haɗa kawunansu wuri guda, su fitar da mutum ɗaya; babu shakka ƙasa za ta ɗauki saiti, domin kuwa hakan zai kasance tamkar wata dabara ce ta fitar da mu daga cikin wannan ƙunci da muke ciki.”
Da yake watsi da batun siyasar yanki da shiyya, Galadima ya ce; “Ban yarda da batun siyasar Arewa da Kudu ba. Mafi cancantar ɗan Nijeriya, ko daga ina ya fito, ko da kuwa daga mafi ƙanƙantar yare ne, shi ya kamata a zaɓa.”
Galadima ya kuma goyi bayan yawaitar jam’iyyu, yana mai cewa; ko kaɗan bai kyautu a tauye yawansu a Nijeriya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp