Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da Sanata Rabi’u Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, a zaben 2023 a kasar Faransa.
Shugabannin biyu sun gana a birnin Paris a ranar Litinin, kuma rahotanni sun ce sun tattauna batutuwan da suka shafi zaben shugabannin majalisar gabanin kaddamar da babban taron kasa karo na 10 a ranar 13 ga watan Yuni.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Tinubu ya bar Nijeriya ne a ranar Laraba, 10 ga watan Mayu zuwa Turai.
Rahotanni sun bayyana cewa zababben shugaban kasar ya shaida wa Kwankwaso cewa ya tuntubi abokan siyasarsa kan bukatar yin aiki tare.
An ce shugaban mai jiran gado da bakon nasa sun amince da gudanar da taruka na gaba.
Yayin da uwargidan Kwankwaso da Abdulmimin Jibrin Kofa, zababben dan majalisar wakilai na NNPP, suka raka shi wurin taron, uwargidan Tinubu da Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai mai barin gado, na daga cikin wadanda suka halarci taron.
“Zababben shugaban kasa da Sanata Kwankwaso sun yi ganawar sama da sa’o’i hudu a birnin Paris ranar Litinin. Taron wanda aka fara da misalin karfe 12:30 na rana ya kare da misalin karfe 4:45 na yamma. Taron ya samu halartar shugaban majalisar wakilai Hon Femi Gbajabiamila.
Zababben dan majalisar wakilai daga Kano, Hon Abdulmumin Jibrin ne ya raka Kwankwaso,” in ji rahoton.
“Sanata Oluremi Tinubu ita ma ta je wajen taron, inda ta tarbi matar Kwankwaso, Hajiya Salamatu, wacce ta zo da mijinta. Tattaunawar ta ta’allaka ne kan doguwar abota da suka yi tun zamanin da suka yi a Majalisar Dokoki ta kasa a shekarar 1992, hadin kan kasa da ci gaban kasa, abubuwan da suka sa a gaba ga sabuwar gwamnati, fafatawar ‘yan majalisun kasa da kuma shirin da zababben shugaban kasa ya yi na kafa gwamnatin hadin kan kasa da Kwankwaso ya yi a baya.”
Majiyar ta ce Tinubu ya kuma yi tsokaci kan sasanta Gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Kwankwaso.
Ganduje ya gaji Kwankwso ne a 2015, amma ‘yan siyasar biyu sun yi hannun riga da juna.