A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawarsa ta farko da gwamnonin jihohi 36 na tarayyar kasar nan a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Laraba.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnonin Zamfara, Kano, Taraba, Kogi, Ogun, Nasarawa, Bayelsa, Adamawa, Ebonyi, Legas, Ribas, Osun, Jigawa, Benuwe, Taraba, Delta, Enugu, Oyo, Filato, Kebbi, Abiya, Imo da kuma Bauchi.
- Tinubu Ya Rantsar Da Akume A Matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya
- Sin Ta Gabatar Da Kakkarfan Korafi Ga Iaea Game Da Shirin Japan Na Zubar Da Gurbataccen Ruwan Tashar Nukiliyar Fukushima Cikin Teku
Mataimakan gwamnonin jihohin Edo da Neja ne ke wakiltar shugabanninsu.
Sauran wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da sabon sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume da aka rantsar.
Idan dai za a iya tunawa, shugaba Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaba a jam’iyyar APC mai mulki a ranar Juma’ar da ta gabata.
Cikakken bayani na tafe…