Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan hatsarin kwale-kwalen da ya faru a Jihar Kwara, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa hatsarin kwale-kwalen ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 da suka halarci daurin aure a kauyen Egbu da ke karamar hukumar Patigi a jihar.
- Daular Sakkwato Ta Buga Littattafan Malaman Musulunci Miliyan 3.2 —Sarkin Musulmi
- An Daure Wata Mata Kan Yi Wa Yaro Dan Shekara 8 Fyade
“Na yi matukar bakin ciki da labarin hatsarin kwale-kwalen da ya lakume rayukan al’ummarmu a Jihar Kwara, kasancewar wadanda abin ya shafa baki ne a wajen wani daurin aure.
“Ina jajanta wa iyalai da abokan arziki da wannan mummunan hatsarin ya rutsa da su. Ina kuma jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Kwara bisa afkuwar hatsarin, da fatan dukkan za su dauki dangana game da wannan hatsari,” in ji shugaba Tinubu.
Yayin da ya bukaci gwamnatin Jihar Kwara da hukumomin gwamnatin tarayya da abin ya shafa da su duba halin da ake ciki a hatsarin jirgin ruwa.
Shugaba Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta duba kalubalen da ke tattare da tafiya a ruwa cikin kasar nan domin tabbatar da cewa lamarin tsaro da aiki ya tabbata.
“Ya kamata gwamnatin Jihar Kwara da hukumomin tarayya da abin ya shafa su hada kai don gano musabbabin faruwar wannan mummunan hatsarin da ya faru.
“Ya kamata kuma a ba da agajin gaggawa da taimako ga wadanda suka tsira da rayukansu da iyalan wadanda abin ya shafa,” in ji shugaban.