Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro saboda kuɓutar da ɗalibai 100 da aka sace daga Makarantar Katolika ta Papiri a Jihar Neja
Ya bayyana farin cikinsa kan dawowar ɗaliban lafiya, amma ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta ceto sauran ɗalibai 115 da malamansu da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga.
- Za A Fara Gasar Wasanni Ta Nakasassu Da Masu Bukata Ta Musamman Ta Sin
- Salah Ba Ya Cikin ‘Yan Wasan Liverpool Da Za Su Kara Da Inter Milan
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya tabbatar wa iyayen ɗaliban cewa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Neja na aiki tare don dawo da dukkanin sauran ɗaliban gida.
Tinubu ya ce dole ne a ceto duk ’yan Nijeriya da aka sace, kuma gwamnati za ta ci gaba da aiki da jihohi don inganta tsaro a makarantu.
Ya kara da cewa jami’an tsaro tare da gwamnonin jihohi dole su hana sace ɗalibai, domin yara su samu damar yin karatu cikin tsaro ba tare da tsoro ba.














