Shugaba Bola Tinubu, ya damu matuka kan yadda wutar lantarkin Arewacin Nijeriya ta lalace wanda hakan ya yi sanadin rasa wuta na sama da mako guda.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkar yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin.
- Jami’an Kiwon Lafiya Na Mozambique Sun Koma Gida Bayan Halartar Horon Samun Kwarewa A Kasar Sin
- Jami’an Kiwon Lafiya Na Mozambique Sun Koma Gida Bayan Halartar Horon Samun Kwarewa A Kasar Sin
Onanuga ya ce abin damuwa ne matuka ganin yadda ‘yan yankin na ci gaba da kasancewa cikin duhu kuma hakan na Æ™ara kassara harkokin kasuwanci da tattalin arziki.
Tinubu, ya ce ya jagoranci wani zama da ministan lantarki don ganin sn gyara wutar cikin gaggawa.
Ya bukaci ministan lantarki da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta kammala aikin gyaran wutar.
“Na damu matuka kan rahotannin lalata layin lantarki da sauran abubuwa da suka janyo rahin wuta,” in ji Tinubu.
Tinubu ya yi kira ga kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya (TCN) da ya yi kokari wajen ganin an gyara wutar cikin kankanin lokaci.
Ya ce gwamnati ba za ta lamunci ci gaba da yin zagon kasa da kuma lalata turakun wutar lantarki ba.
Mazauna yankin na ci gaba da bayyana damuwarsu kan yadda aka shafe tsawon lokaci babu wutar lantarki.