Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga a sake duba farashin kuɗin aikin Hajjin 2026, domin rage nauyin da zai rataya kan alhazai, sakamakon yadda Naira ke ƙara ƙarfafa kan Dalar Amurka a kasuwa.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya mika umarnin Shugaban ƙasan ga Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), inda ya ce a cikin kwanaki biyu hukumar ta fitar da sabon tsarin farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar yanzu.
- EFCC Ta Kama Daraktocin NAHCON 2 Kan Zargin Karkatar Da Kuɗin Hajjin 2025
- Hajji: Kawo Yanzu An Kammala Jigilar Maniyyatan Jihohi 12 A Nijeriya – NAHCON
Da yake jawabi a fadar shugaban ƙasa bayan taro da shugabannin NAHCON, Shettima ya ce ya zama dole a samu hadin kai tsakanin gwamnoni da jami’an hukumar alhazai domin tabbatar da tsarin farashi mai sauƙi da adalci ga maniyyata.
A cewar Sanata Ibrahim Hadeija, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, burin gwamnati shi ne rage kuɗin da maniyyata ke biya saboda sauye-sauyen tattalin arzikin da ke faruwa sakamakon gyare-gyaren gwamnati.
Shi ma Sakataren NAHCON, Dr Mustapha Mohammad, ya ce wannan mataki na shugaban ƙasa zai ƙara yawan maniyyata a bana, yana mai jaddada cewa “ƙarancin farashi zai ba da damar musulmi da dama su sami damar aiwatar da wannan rukuni mai muhimmanci na addinin Musulunci.”