Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN).
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin kasa, Mista Godwin Emefiele, daga aiki ba tare da bata lokaci ba,” in ji daraktan yada labaran gwamnatin tarayya, Willie Bassey a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
- Dawowar Ta’addanci Ta Sake Jefa Sakkwatawa Da Zamfarawa Cikin Zullumi
- Alfanu Da Rashin Alfanun Rusau A Kano Daga Bakin Kanawa
“Wannan ya biyo bayan binciken da ake yi a ofishinsa da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a bangaren hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar nan.
“An umarci Mista Emefiele da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Mataimakin Gwamnan na bangaren Ayyuka wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan Babban Bankin kasar nan har sai an kammala bincike da kuma gyara.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp