Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan Malam Kabir Yusuf, wani gogaggen ɗan Jarida da ya rasu a jiya Talata. Malam Yusuf ya yi suna a matsayin wakilin babban birnin tarayya na Jaridar Triumph da Rediyon Faransa. Ya kuma shafe shekaru da dama yana aiki a gidan gwamnati.
A cikin sakonsa, shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan Malam Yusuf, ya kuma yi wa iyalansa ta’aziyya a wannan lokaci na jimanin rashinsa.
- Shehun Borno Ya Bukaci Tinubu Ya Kwato Kananan Hukumomin Da Ke Hannun ‘Yan Boko Haram
- Ƴan Ta’addan Da Suka Kai Hari Borno Zasu Yabawa Aya Zaƙinta – Tinubu
Ajuri Ngelale, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman ne ya fitar da sanarwar a yau 3 ga Yuli, 2024.
Talla