Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sababbin naɗe-naɗe takwas na shugabannin hukumomin da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Ƙasa, Mista Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Alhamis.
- ‘Yan Jarida Sun Cancanci Samun Rayuwa Mai Inganci A Nijeriya – Minista
- Za Mu Dasa Wa ‘Yan Nijeriya Dabi’ar Gaskata Kalaman Shugabanni A Zukatansu – Minista
Sanarwar ta bayyana cewa an naɗa Mista Lanre Issa-Onilu a matsayin Shugaban Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA); Alhaji Salihu Abdulhamid Dembos a matsayin Shugaban Gidan Talbijin na Nijeriya (NTA), da Dakta Muhammad Bulama a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Rediyon Tarayya na Nijeriya (FRCN).
Ita kuma Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talbijin ta Ƙasa (NBC), an naɗa mata Mista Charles Ebuebu a matsayin shugaba, yayin da aka naɗa Alhaji Jibrin Baba Ndace a matsayin Shugaban gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON).
Haka kuma an naɗa Dakta Lekan Fadolapo matsayin Shugaban Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON), da Malam Ali M. Ali a matsayin Shugaban Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), sai Hukumar Kula da Gidajen Jaridu ta Ƙasa (NPC) wadda aka naɗa Dili Ezughah matsayin shugaban ta.
Shugaba Tinubu ya hori waɗannan sababbin shugabannin da cewa su ƙirƙiro tare da bijiro da sababbin fasahohi da damarmakin da ‘yan Nijeriya za su amfana, ta yadda za a ci moriyar canji a hukumomin domin ƙarfafa haɗin kai a ƙasar nan.
Ya ce ta haka za su bayar da gagarumar gudunmawar ɗaukaka Nijeriya har ta yi goyayya da manyan ƙasashen duniya.
Sanarwar ta ce naɗin nasu ya fara aiki nan take.