Shugaba Bola Tinubu, ya naɗa Muhammad Babangida, ɗan tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, a matsayin shugaban Bankin Manoma na Ƙasa (BOA).
Sanarwar hakan ta fito ne daga mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, a ranar Juma’a.
- ‘Yan Kasuwa Na Shirin Yi Wa Dangote Zanga-zanga Kan Rage Farashin Gas
- Ko Kaɗan Bamu Ji Takaicin Ficewar Atiku Daga Jam’iyyar PDP Ba — Damagum
Ya kuma naɗa sabbin shugabanni a wasu hukumomin gwamnati takwas.
Muhammad Babangida ya yi karatu a Jami’ar Turai da ke Switzerland, inda ya samu digiri a harkar kasuwanci da kuma digirin digirgir a hulɗa da jama’a.
Ya kuma yi kwasa-kwasai da suka shafi shugabanci a makarantar kasuwanci ta Harvard a 2002.
Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Lydia Kalat Musa daga Kaduna, Jamilu Wada Aliyu daga Kano, Yahuza Ado Inuwa daga Kano, Sanusi Musa daga Kano.
Sauran sun haɗa da Farfesa Al-Mustapha Alhaji Aliyu daga Sakkwato, Sanusi Garba Rikiji daga Zamfara, Tomi Somefun daga Oyo da Dr Abdulmumini Mohammed Aminu-Zaria daga Kaduna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp