Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan karin Naira tiriliyan 2.7 na kasafin kudi.
In ba a manta ba, majalisar dattawa da ta wakilai, a ranar Alhamis din da ta gabata, sun amince da karin kasafin kudi na naira tiriliyan N2.17trn na shekarar 2023.
- Yadda Aka Gudanar Da Gasar Adabi karo Na Uku Don Bunƙasa Ilimin ‘Ya’ya Mata A Katsina
- Bashin Da Ake Bin Nijeriya Ya Haura Tiriliyan N89.3
Shugaba Tinubu ya rubutawa Majalisar Dokoki ta kasa takardar neman amincewa da Naira Tiriliyan 2.17 a matsayin karin kasafin kudin shekarar 2023 don kari da gyare-gyaren albashin ma’aikata.
Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) da shugaban kasa ya jagoranta a ranar Litinin ta amince da karin kasafin kudin shekarar 2023 na Naira tiriliyan 2.17.
Wadanda suka halarci rattaba hannun akwai shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio; Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas; Shugaban ‘yan Majalisar Dattawa, Sen Opeyemi Bamidele; Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kudi, Sen Olamilakan Adeola; Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Bichi.
Sauran sun hada da Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume; Ministan Kasafin Kudi, Atiku Bagudu da Shugaban Hukumar tattara harajin cikin gida na gwamnatin Tarayya, Zachs Adedeji.