A cikin watan Satumbar wannan shekarar, Gwamnatin tarayya ta fitar da sama da Naira biliyan 29, domin a inganta manyan hanyoyin kasar nan, tare da kuma bunkasa hanyoyin ruwa wanda ma’aikayar ayyuka ta tarayya, ke jagoranta.
A cewar wasu bayanai da aka samo a kafar sada zamunta ta gwamnatin, wani kamfanin cikin gida na BudgIT ne, aka bai wa kwangilar aikin.
- Daga Yanzu Saudiyya Ce Za Ta Kula Da Abincin Alhazan Nijeriya -NAHCON
- Wakilin Sin: Ya Kamata A Kiyaye Da Karfafa Gudummawar MDD A Fannin Yaki Da Ta’addanci
Wasu daga cikin kudaden da aka fitar sun hada da; Naira biliyan 5.88, da aka bai wa kamfanin Reinforced Global Resources Ltd kwangilar aikin gyran babbar hanyar Ugep-Opkosi wacce ta hada da jihar Koros Ribas da jihar Ebonyi .
Kazalika, an kuma bai wa kamfanin JRB Constructions Company Ltd kwangilar Naira biliyan 4.42 don gyran babbar hanyar Potiskum-Jakusko-Gashua da ke a jihar Yobe.
Kwangilayr yin sabuwar hanyar Maraba Donga da ke a jihar Taraba, an baiwa kamfanin Rockborough DL Prime Ltd Naira biliyan 1.26 don yin aikin, inda kuma aka bai wa kamfanin .Truetech Global Inbestment Serbices Ltd Naira biliyan 1.25 don yin aikin babbar hanyar Gabas maso yamma da ke a jihar Delta.
Bugu da kari, na kuma bai wa kamfanin HMF Construction Ltd Naira biliyan 1.04 domin ayyukan manya hanya da ban da ban na Abeokuta-Ajebo da ke a jihar Ogun.
A jihar Sokoto kuma, an bai wa kafanin Sholly Frontlink Impec Ltd Naira biliyan 567.37. don yin aikin manyan hanyoyin Aliero, inda kuma aka bai wa kamfanin Logine International Ltd, Naira miliyan 780.98 domin yin murafan magudana.
A bangaren aikin samar da ruwa sha kuwa, an ware Naira miliyan 905.24, domin a kammala Dam din Farin Ruwa da ke a karamar hukumar Wamba a jihar Nasarawa, inda aka bai wa kafanin Wiz China Worldwide Engineering Ltd kwangilar yin aikin.
An kuma kara ware wasu karin Naira miliyan N678.16 a ,matsayin kudin hadaka na wanda yake da kaso 50, na aikin samar da ruwan sha a karkashin Asusun bayar da tallafi na kananan yara na majalisar diinkin duniya.
Bugu da kari, bayanna sun nuna cewa, gwamnatin ta bai wa kamfanin Medabille Construction Ltd Naira biliyan 1.90 don yin aikin gina wasu sabbin sakarariya a jihar Kebbi tare da kuma bai wa kamfanin Candon Construction Ltd, Naira biliyan 1.82 don gina sakatariya ta tarayya a jihar Abia tare da kuma bai wa kamfanin Strabic Construction Ltd, Naira biliyan1.82 don gina wata sakatriyar a jihar to Ebonyi.
An kuma bai wa kamfanin Steady Lane Nigeria Ltd Naira biliyan 1.49 don gina sakatariya a garin Lokoja da ke a jihar Kogi.
Sauran ayyukan gyran manyan hanyoyin, an bai wa kamfanin Rockborough DL Prime Ltd Naira biliyan 1.23, don gyran babbar hanyar Zamfara, an kuma bai wa kamfanin Gerawa Global Engineering Ltd Naira miliyan 596.36 a matsayin kafin Alkami na aikin babbar hanyar jihar Borno, inda kuma aka bai wa kamfanin Anbez Innobations Ltd, Naira miliyan 511.07 domin gyran babbar hanyar Katsina zuwa Daura.