Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tafi Faransa a sabon jirgin Airbus A330 da aka saya masa a cewar fadar shugaban kasa.
Jirgin ya maye gurbin tsohon da shugabannin Najeriya suka kwashe shekaru 19 ana amfani da shi in ji Kakakin Tinubu Bayo Onanuga.
- Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Karuwar Zargin Cin Zarafi A Rundunar Sojojin Amurka
- Karfafa Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Vietnam
“Wannan sabon jirgi da aka sayo a farashi mai rahusa, ya sa Najeriya za ta kauce wa kashe miliyoyin daloli wajen gyara da sayen mai a kowace shekara.” Onanuga ya ce a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Litinin.
Tun a zamanin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo ake amfani da tsohon jirgin a cewar shi.
Maye gurbin tsohon jirgin mai lamba B737 – 700 (BBJ) ya biyo bayan zaman jin bahasi da majalisar dokokin Najeriya ta yi kan lafiyar jirgin da kuma kudin gyaransa, “musamman bayan da ya lalace yayin wata tafiya da aka yi da shi zuwa Saudiyya.”
Sabon jirgin ya iso Abuja ne, daren ranar Lahadi, bayan kamfanin China da ya sa kotu ta kwace shi, ya amince ya saki guda daya da zai kai shugaba Tinubu Faransa.
Jirgin kirar 330 na daga cikin kadarorin wani attajirin da ke harkar mai ya mika shi ga bankin Jamus, a matsayin jinginar karbar lamuni, daga bisani kuma aka sayar da shi.
Bayanai sun ce wani kamfanin sufurin jiragen Amurka da ake kira L&L da ke Miami Florida ne, ya jagoranci yarjejeniyar sayar wa Nijeriya jirgin a kan sama da dala miliyan 100.
Wasu rahotanni sun bayyana cewar Nijeriya ta samu jirgin a farashi mai sauki domin a yanzu farashinsa ya kai Dala miliyan 600.
Kasaitaccen jirgin na alfarma yanzu ya zama jirgin shugaban kasa da ake kira ‘Nigeria Air Force One’ mai lamba 5N-NGA.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa, ta ce sabon jirgin ya ci kudinsa saboda kayan alatun da ke ciki da kuma inagancinsa la’akari da girma da kuma kimar shugaban Nijeriya a idon duniya.
A baya dai an tafka mahawara a kan muhimmancin sauyawa shugaban kasa jirgi, ya yin da babu wani bayani daga fadar shugaban kasa dangane da wannan ciniki.
A baya’yan Nijeriya sun bayyana bacin ransu dangane da bukatar sayen sabon jirgin da Tinubu ya yi.