Shugaba Bola Tinubu, ya taya Donald Trump murnar zama shugaban kasar Amurka na 47.
A cikin wata sanarwa ta hannun mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce Tinubu ya yi masa fatsn alheri.
- Kotu Ta Hana CBN Da Sauransu Yi Wa Kudaden Kananan Hukumomi Katsa-Landan
- Zaben Amurka: Trump Na Kan Gaba Yayin Da Aka Ci Gaba Da Kirga Kuri’u
Sannan ya bukaci dangantaka tsakanin Nijeriya da Amurka, ta kara karfi musamman game da batutuwan tattalin arziki, zaman lafiya, da kalubalen duniya.
Tinubu ya bayyana nasarar Trump a matsayin zakaran gwajin dafi bayan da ‘yan Amurka suka aminta da jagorancinsa.
Ya bayyana cewa dawowar Trump a matsayin shugaban kasar za ta kawo ci gaba da hadin kan kasashen Afirka, tare da taimakawa wajen samar da zaman lafiya da wadata a duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp