Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tsawaita zaman sa a Turai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Wannan ya biyo bayan zarge-zarge daga jam’iyyar adawa ta PDP da wasu shugabannin adawa, waɗanda suka fara tambayar dalilin rashin dawowar shugaba ƙasa a lokacin da ƙasar ke fuskantar matsaloli a sassa daban-daban.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci shugaban ya dawo gida, yana mai zargin cewa halin da ake ciki a jihohin Filato, Benuwe da sauran sassan Nijeriya yana buƙatar cikakken hankalin shugaban.
- Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa
- Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna
A ranar 2 ga Afrilu, jirgin Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa Paris, Faransa, a kan ziyara ta aiki, kamar yadda ofishin shugaban kasar ya bayyana. An bayyana cewa, a cikin wannan ziyarar, shugaban zai duba yadda gwamnatinsa ta gudanar da aiki da kuma yin nazari kan muhimman matakai na ci gaba.
A yayin da yake ƙasar Faransa, Tinubu yana ci gaba da hulɗa da tawagarsa, yana kuma kula da harkokin gwamnati, ciki har da bayar da umarni ga jami’an tsaro kan barazanar da ke tasowa a wasu sassan ƙasar.
Sai dai, yayin da ake ci gaba da zarginsa, PDP ta bayyana cewa tafiyar tana nuni da rashin kulawa da aikace-aikacen gwamnati. Wakilin jam’iyyar, Abdullahi Ibrahim, ya bayyana cewa ziyarar tana nuna rashin kulawa da aikin gwamnati, yana mai cewa shugaban ƙasar ba ya damuwa da halin da al’umma ke ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp