Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta ceto sauran mata daliban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a ranar Juma’a.
Da ya ke Allawadai da garkuwa da daliban, shugaban kasa acikin wata sanarwa da kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce, babu wani dalilin da zai sanya masu garkuwan su sace wadanda ba su ji ba su gani ba, kawai laifinsu shi ne don suna neman ilimi mai inganci, ya ce, wannan lamarin ba abun lamunta ba ne sam.
- Gwamnatin Kaduna Ta Nemi Saudiyya Ta Zuba Jari A Jiharta
- Masu Yi Wa Kasa Hidima 8 Da Aka Sace Sun Shafe Kwanaki 32 A Hannun Masu Garkuwa A Zamfara
Yayin da shugaban kasan ya jajanta wa iyalan wadanda wannan lamarin ya shafa, ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na yin aiki tukuru domin kare rayuka da dukiyar kowani dan Nijeriya.
A kan wannan aniyar, Tinubu ya bai wa iyalan wadanda aka yi garkuwa da su tabbacin cewa, gwamnati za ta yi dukkanin abunda ya da ce domin ganin daliban sun dawo cikin koshin lafiya.
Bugu da kari, shugaban ya sha alwashin cewa, gwamnatin tarayya za ta tabbatar da cewa cibiyoyin ilimi sun cigaba da kasancewa wuraren samar da ilimi, sannan kuma an karesu daga aikace-aikacen ‘yan ta’adda.