Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunan duk wani jami’i da zai je taron ba tare da wata hujja ba ta shiga kai-tsaye cikin jadawalin ayyukan UNGA da aka tsara ba.
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ta dakatar da ba da biza ga jami’an gwamnati da ke neman damar zuwa birnin New York na Amurka don halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya UNGA na bana.
- Yawan Sinawa Masu Amfani Da Intanet Ya Kai Fiye Da Biliyan 1
- Tattalin Arzikin Nijeriya Na Bukatar Ingantawa Cikin Gaggawa – Tinubu
A sanarwar da kakakin shugaban kasar Ajuri Ngelale ya fitar ranar Litinin, Tinubu ya ce an dauki matakin ne don rage kudaden da gwamnati ta ke kashewa a kan tafiye-tafiyen jami’anta.
Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunan duk wani jami’i da zai je taron ba tare da wata kwakkwarar hujja ba.
“Don takaita duk wani tsaiko da ka iya biyo bayan wannan umarni, Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya da ke aikin ba da biza tare da babban ofishin da ke birnin New York, za su yi aiki tare wajen tabbatar da an bi matakan da suka dace wajen tantance wadanda za su je taron a hukumance,” in ji sanarwar.
Bisa ga wannan umarni na shugaban, an bukaci duk wata ma’aikata ta tarayya da hukumomi su tabbatar da cewa sun takaita yawan jami’ansu da suka saka a cikin tawagar da za ta halarci taron na UNGA.
Kazalika, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa daga yanzu dole jami’an gwamnati su dinga taka-tsantsan wajen tafiyar da kudaden al’umma da ake kashewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp