Bola Ahmed Tinubu, zababben shugaban kasa ya bayyana cewa ‘yan fashi, ta’addanci da kashe-kashen hankali bai kamata su zama wurin zama a Nijeriya ba.
Ya bayyana ra’ayinsa ne kan hare-haren da ‘yan bindiga da mahara suka kai a karamar hukumar Maru a Jihar Zamfara a karshen mako da kuma garin Maigari da ke karamar hukumar Rimin Gado a Jihar Kano.
- Ka Daina Gararamba A Titi Ka Tafi Kotu —Martanin APC Ga Atiku
- Ba Za Mu Bari NNPP Ta Yi Magudin Zabe A Kano Ba —Gwamnatin Kano
Tinubu ya bayyana cewa an kashe jami’in ‘yan sanda da dan banga a harin da ‘yan bindiga suka kai a Zamfara.
“A harin na Kano, ‘yan bindiga sun kutsa gidan wani basarake inda suka harbe shi har lahira,” in ji zababben shugaban kasar.
Ya kara da cewa harin da aka kai garin Maru bayan an samu zaman lafiya a Zamfara, ya kara da cewa akwai bukatar a kara kaimi domin murkushe ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda gaba daya.
“A matsayinmu na kasa dole ne mu hada kai domin mu fatattaki wadannan ‘yan ta’addanci gaba daya. Kashe-kashen rashin hankali da ta’asa irin wannan bai kamata su kasance a kasarmu ba,” in ji shi.
Ya jajantawa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mista Usman Baba, da gwamnatin Zamfara da iyalan jami’an tsaron da abin ya shafa game da rasuwar.
Tinubu ya kuma bukaci a gudanar da bincike kan kisan Hakimin Maigari a Jihar Kano, wanda shi ne mahaifin Shugaban karamar Hukumar Rimin Gado, Mista Munir Maigari.
Ya mika ta’aziyyarsa ga shugaban karamar hukumar, da gwamnatin Jihar Kano da kuma iyalan marigayin bisa mummunan kisan da aka yi wa shugaban al’umma.
A cikin sakon ta’aziyya daban-daban, zababben shugaban kasar ya jajanta wa fitaccen malamin nan Sheikh Ahmad Gumi da ya rasa mahaifiyarsa da kuma iyalan marigayi Janar Sani Abacha bisa rasuwar dansu Abdullahi.
“Akwai kuna rabuwa da masoyi komai yanayi da shekaru.
“Ba za mu iya tambayar Allah ba, sai dai kawai mu yi addu’a Allah Ta’ala ya jikansu, ya kuma ba mu karfin jure wa rashinsu,” in ji shi.