A wani yunkuri na magance matsalolin da masana’antu da sauran masu ruwa da tsaki suka nuna dangane da sauye-sauyen haraji na baya-bayan nan, Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan wasu umarnin zartarwa guda uku na dakatar da manyan matakan haraji.
Matakin ya zo ne a matsayin mayar da martani ga bukatar daidaita haraji, kamar yadda aka ayyana a cikin Tsarin Harajin Kasa na 2017.
- Kamfanin Meta Mamallakin Facebook Ya Yi Wa Twitter Kishiya
- Bincikenmu Ya Nuna Bidiyon Dalar Ganduje Gaskiya Ne –Muhyi
Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan ayyuka na musamman da sadarwa, Dele Alake ne, ya bayyana hakan a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis.
Dokar zartarwa ta farko da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu ita ce Dokar Kudi ta 2023. Y
Ya jinkirta aiwatar da canje-canjen da aka tsara a cikin Dokar daga Mayu 23, 2023, zuwa 1 g watan Satumba 2023, inda zai tabbatar da bin ka’idojin da aka tsara.
Ya kuma yi sauye-sauye dangane da harajin da Kwastam ke karba.
Bugu da kari, shugaba Tinubu ya bayar da umarnin dakatar da harajin kashi 5% na ayyukan sadarwa, da kuma karin haraji kan kayayyakin da ake kerawa a cikin gida.
Alake ya ce matakin ya nuna aniyar Tinubu na samar da kyakkyawan yanayi na kasuwanci da kuma rage wahalhalun da ‘yan kasuwa da jama’a ke fuskanta.
Shugaban ya kuma bayar da umarnin dakatar da sabon haraji kan robobin da ake amfani da su da suka hada da kwantena da kwalabe.
Alake ya kuma ce an dakatar da biyan harajin shigo da kaya a kan wasu motoci.
A cewarsa, manufar shugaba Tinubu ita ce ya saurari damuwar al’ummar Nijeriya tare da rage radadin da ke tattare da haraji, maimakon ta’azzara kalubalen da ‘yan kasar nan ke fuskanta.