Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya aika da sakon ta’aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Namadi.
Hajiya Maryam, ta rasu a ranar Laraba, 25 ga watan Disamba, 2024 kuma an yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin Kafin Hausa, mahaifar gwamnan.
- Mutum 2 Sun Mutu Yayin Da ‘Yansanda Suka Ceto Mutum 10 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Katsina
- Mota Ta KaÉ—e Masu Tattakin Kirsimeti 22 A Gombe
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu ya yaba wa Hajiya Maryam kan hidimar da ta yi wa al’umma.
Ya kuma karfafa wa iyalinta gwiwa su ci gaba da ayyukan yin alherin da ta yi domin girmama tarihinta.
Shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga Gwamna Namadi da iyalansa da su kasance masu haƙuri game da wannan rashi.