Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun sanar da shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 a hukumance, yayin zaman haɗin gwuiwa da aka shirya gudanarwa a ranar Juma’a.
Sanarwar na ƙunshe ne a wata wasiƙa da Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya karanta a zauren majalisar a ranar Alhamis, inda shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta makamanciyar wasiƙa a zauren Majalisar Dattawa.
- Kamfanonin Sin Da Zimbabwe Za Su Yi Hadin Gwiwa Wajen Kera Na’urorin Wutar Lantarki
- Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Sun Jima Suna Kitsa Karairayi
A cewar wasiƙar, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, zai gabatar da daftarin kasafin shekarar 2026 da misalin ƙarfe 2 na ranar Juma’a, tare da sa ran zaman zai koma zauren Majalisar Wakilai da misalin ƙarfe 1:45 na rana.
A wani ɓangare kuma, Majalisar Dattawa ta karɓi wasiƙu biyu daban-daban daga Shugaban Ƙasa Tinubu, inda yake neman tabbatar da naɗin shugabannin hukumomin kula da harkokin man fetur, bisa tanade-tanaden Dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 (PIA).
A wasiƙar farko, Shugaban Ƙasa ya nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Injiniya Saidu Muhammad, a matsayin Babban Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta ƙasa (NMDPRA), bisa sashe na 41(6) na PIA 2021, yana mai bayyana cewa wannan naɗi ya biyo bayan murabus ɗin tsohon Babban Shugaban hukumar.
Ya jaddada buƙatar kaucewa giɓi a shugabancin hukumar, duba da rawar da muhimmancinta wajen kula da ayyukan da suka jiɓanci man fetur da izinin zirga-zirgarsa a jiragen ruwa.
A wasiƙa ta biyu kuma, Shugaban Ƙasa ya nemi tabbatar da naɗin Mista Oritsemanori Sewa Inyosa, a matsayin Babban Shugaban Hukumar Kula da bayar da lasisin dakon man fetur zuwa ƙasar nan (NUPRC), bisa sashe na 11(3) na Dokar PIA 2021, inda dukkan naɗe-naɗen aka miƙa su ga Kwamitin Majalisa domin gaggauta duba su tare da yiwuwar amincewa.














