Bayan an rantsar da gwamnatin zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayu, ,gwamnatinsa za ta sanya sabuwar ranar da za a yi kidayar ‘yan Nijeriya.
An ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da dage kidayar ta 2023 wadda aka kebe za a gudanar daga ranar 3 zuwa ranar 7 ga watan ga watan Mayu 2003, amma a yanzu sabuwar gwamnatin mai zuwa, za ta sa sabuwar ranar da za a yi kidayar.
- Har Yanzu Wasu Na Yi Wa ‘Yan Fim Kallon Mutanen Banza —Auwal West
- Sarkin Da Ya Fi Dadewa A Karagar Mulki Ya Rasu
A cikin sanarwar da ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar “Buhari ya dage yin kidayar ne, bayan ya ganawar da ya yj a Abuja da wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwa cikinsu har da shugaban hukumar kidaya ta kasa da tawagarsa.
Mohammed ya ce, “A ganawar an jaddada mhhimmanci yin kidayar ta al’ummar kasar da kuma kidaya gidajen al’ummar kasa bayan an shafe shekaru 17 ba a yi kidayar ba.
“Yin kidayar zai bayar da dama wajen samun bayanan ‘yan Nijeriya, inda hakan zai taimaka wa gwamnati wajen kara inganta rayuwarsu.”
An ruwaito cewa, shugaban hukumar a wata ganawa a ranar Alhamis da ta wuce da wasu jakadun ketare a Abuja ya sanar da cewa, har yanzu hukumar ba ta samu daukacin kayan da ta ke bukata don gudanar da kidayar ba.
Sai dai, shugaban ya bayyana cewa, a ‘yan kwanaki masu zuwa, za a samar da kayan aikin yin kidayar, inda ya ce, Nijeriya na bukatar a samar da kananan Kwamfuta guda 800,000 wadda a yanzu aka riga aka samar da guda 500,000.
Hakazalika, an ruwaito daraktan kula al’amuran yau da kullum na hukumar Dakta Isiaka Yahaya ya ce, an dage yin kidayar ne ba dan rashin kudi ba, amma gwamnatin mai zuwa, za ta gudanar da yin kidayar.