Shararren dan wasan tsakiyar Real Madrid da Kasar Jamus, Toni Kroos, ya bayyana cewar zai yi ritaya daga kwallon kafa da zarar an kammala gasar Euro ta 2024.
Dan wasan ya shafe shekaru 10 a Real Madrid tun bayan da kungiyar ta saye shi a shekarar 2014 daga Bayern Munich.
- Ƴansanda Sun Dakile Hari, Sun Ceto Mutane A Abuja
- Sanata Barau Jibrin Ya Ƙaddamar Da Motocin Zirga-Zirga A Kano
Kroos ya buga wa Madrid wasanni 463 tare da lashe kofuna 22.
Tuni Real Madrid ta fitar da sanarwa a shafinta ja Intanet, inda ta yi wa dan wasan godiya da jinjina kan tsawon lokacin da ya shafe a kungiyar tare da kafa tarihi.
A wannan shekara an sha kai ruwa kan batun ko dan wasan zai sake rattaba hannu a kungiyar don ci gaba da zama kamar yadda Luka Modric ya yi.
Sai dai daga karshe, Kross ya zartar da hukuncin kan jingine takalmansa da zarar an kammala gasar Euro ta bana.