Tottenham Ta Yi Wa Harry Kane Farashin Fam Miliyan 150

Harry Kane

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham za ta bukaci zunzurutun kudi har Fam miliyan 150 a kan dan wasanta na gaba, Harry Kane, a cinkin tsabar kudi kawai, ba tare da an hada mata da wani dan wasa ba, kamar yadda rahotanni suka ruwaito.

Wannan ka’ida na zuwa ne a yayin da Manchester City ta bayyana aniyar mika wa Tottenham manyan ‘yan wasanta guda biyu da suka hada da Raheem Sterling da Gabriel Jesus domin kai wa gaci a cinikin.

Kane na daya daga cikin ‘yan wasan da aka fi nema  da ke kasuwa a halin yanzu, bayan da ya saka kwallaye 23, ya kuma taimaka aka ci 14 a kakar da aka karkare kwanan nan a firimiyar kasar Ingila.

Exit mobile version