Mark Zuckerberg ya gana da Donald Trump a liyafar cin abincin dare a ranar Laraba, a gidansa da ke Mar-a-Lago a Florida na kasar Amurka.
Ganawar na zuwa a daidai lokacin da mamallacin kamfanin Meta, Mark Zuckerberg ke kokarin kyautata alaka da zababben shugaban.
- Liverpool Ta Sake Nuna Barakar Real Madrid A Anfield
- Tattalin Arziki: Gwamna Lawal Ya Nemi Hadin Gwiwar Masu Zuba Jari Na Kasashen Afirka A Taron AFREXIM A KenyaÂ
Mataimakin daraktan ofishin shugaban kasar, Stephen Miller ne, ya tabbatar da ganawar da mutanen biyu suka yi a gidan talabijin na Fox News.
Ya bayyana cewa shugaban fasahar ya nuna karara cewa yana so ya goyi tsarin Trump na sabunta kasar Amurka karkashin jagorancinsa.
Zuckerberg Shugaban Meta, mamallaka Facebook, “ya nuna goyon bayansa da kuma nuna sha’awarsa na tallafawa da kuma shiga cikin wannan canjin da muke gani a duk faÉ—in Amurka.”
Mark Zuckerberg ya yi godiya da gayyatar da aka yi masa a gidan Shugaba Trump don cin abincin dare da kuma damar ganawa da mambobin tawagarsa game da gwamnati mai zuwa,” in ji mai magana da yawun kamfanin na Meta.
Yayin da suka yi taka tsantsan a lokacin wa’adin farko na Donald Trump, shugabannin fasaha, kamar Elon Musk, sun yi gaggawar maraba da nasarar da ya samu a watan Nuwamba, kuma Mark Zuckerberg na daya daga cikin wadanda suka taya shi murna.
Mark Zuckerberg ya kare ayyukan agajin da ya shafi zabe kuma kamfaninsa na Meta ya kawo gyara.
Shafin Facebook yana daya daga cikin hanyoyin sadarwar zamantakewa da suka haramta wa Donald Trump wallafa ko kuma shiga cikin dandalin bayan harin da aka kai kan Capitol a ranar 6 ga watan Janairun 2021.