Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar sanya ƙarin haraji na kashi 10% kan kowace ƙasa da ta goyi bayan manufofin ƙungiyar BRICS da ke adawa da muradun Amurka. Trump ya bayyana hakan ne ta shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa ba za a samu wani rangwame ba ga kowace ƙasa da ke bin wannan hanya.
Ƙungiyar BRICS, wacce da farko ta ƙunshi ƙasashen Brazil, Rasha, Indiya, China da Afirka ta Kudu, yanzu ta karɓi ƙarin ƙasashe kamar Masar, Habasha, Indonesia, Iran, Saudiyya da haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE). Ƙungiyar na wakiltar fiye da rabin yawan al’ummar duniya kuma tana gudanar da taronta a birnin Rio de Janeiro, inda shugabannin ke kiran a sake fasalin manyan cibiyoyin ƙasa da ƙasa da kuma ƙin amincewa da haraji da ke haddasa taɓarɓarewar tattalin arziƙi.
- Tsarin BRICS Ya Zama Muhimmin Dandalin Hadin Kai Na Kasashe Masu Tasowa
- Tsakanin Nijeriya Da BRICS+: Idan Zamani Ya Dinka Riga…
Wannan barazana daga Trump ta zo ne bayan BRICS ta soki manufofin harajin Amurka da kuma ƙoƙarinta na samar da tsarin kuɗin da zai maye gurbin Dalar Amurka. A cewarsa, irin wannan haɗin gwuiwa barazana ce ga Amurka kuma za ta fuskanci martani mai tsauri.
Masana sun bayyana cewa cire alaƙa da China, wacce ke ɗaya daga cikin manyan mambobin BRICS, ba abu ne mai sauƙi ba saboda tasirinta a fannonin fasahar zamani kamar motoci masu amfani da lantarki, da batir, da albarkatun ƙasa kamar sinadarai masu ɗauke da maganadisu.
Andrew Wilson daga Cibiyar Kasuwanci ta Duniya ya ce: “A aikace, sauya China a waɗannan fannonin yana da matuƙar wahala.” Duk da haka, Trump ya sha alwashin ɗaukar matakan tattalin arziƙi domin kare matsayin Amurka a duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp