Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yana shirin yin magana da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, domin tattauna batun kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Trump ya bayyana haka yayin da yake cikin jirgin shugaban ƙasa, Air Force One, a hanyarsa ta komawa Washington daga Florida.
Ya ce yana ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen wannan rikici kuma an samar da wasu matakai masu muhimmanci a makon da ya gabata.
Trump yana ƙoƙarin samun goyon bayan Putin kan tsagaita wuta na kwanaki 30 da Ukraine ta amince da shi a makon da ya gabata.
Sai dai, duk da wannan yunƙuri, dakarun Rasha da Ukraine sun ci gaba da kai hare-hare, inda sojojin Rasha suka matsa lamba a yankin Kursk.
A ranar Juma’a, fadar Kremlin ta ce Shugaba Putin ya aike saƙo zuwa ga Trump ta hannun manzon Amurka na musamman, Steve Witkoff, yana bayyana cewa Rasha tana nazarin batun tsagaita wuta amma tana taka-tsantsan.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta kai ga samun mafita, amma ya jaddada cewa dole ne Rasha ta mayar da yankunan da ta ƙwace.
Tun a shekarar 2014, Rasha ta ƙwace yankin Crimea, sannan a shekarar 2022 ta mamaye wasu yankuna huɗu na gabashin Ukraine.
Yanzu dai ana fatan wannan tattaunawa za ta kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana ci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp