Connect with us

KIWON LAFIYA

Tsabtace Muhalli Na Fuskantar Kalubale A Nijeriya

Published

on

Alkalumman da aka samu daga Multiple Clustres Indicator Surbey ( MICS) da kuma JMP sun nuna cewar, hanyoyin da ake bi ko kuma amfani dasu, saboda tsafatace muhalli,a Nijeriya abin ya ragu sosai da sosai, tsakanin shekarun 2000 da kuma 2015, sai kuma yadda ake yin kashi ko ta ina aka ga dama wato a waje, abin ya kai intaha ne tsakanin shekaraun 2010 da kuma 2015.
Wani babban jami’ine daga cibiyar kula da asusun yara ta majalisar dinkin duniya, a ani taro nan kana biyu, wanda aka shirya, dangane da muhimmanci tsaftace ruwan sha, ko kuma kulawa da yadda ake samar da shi ruwan , wanda aka yi a jihar Anambra. Mainga Moono Banda ya bayyana cewar kamar ‘yan Nijeriya milyamn 130 ne suka amfana da kayayyakin kula da tsaftace muhalli na zamani, ya kara da cear fiye da rabin su mutanen da suke zama ne a karkara.
Da yake bayyana hakan lokacin da ake taron kwana biyu na ganaa da manema labarai, akan yadda za tsafatce ruwa, wanda aka yi a jihar Anambra (WASH), tun farkoa cikin makon wani kwararre a harkar bincike daga asusun yara na majalisr dinkin duniya, Mainga Moono Banda, ya bayyana cewar da yake an samu koma bayan tsaftace muhalli, a Nijeriya, kasar zata samu matsawla wajen kokarin data ke yi, wajen cimma burin a muradan ci gaba na Sustainable Debelopment Goal (SDG) akan tsafatce ruwa, ai dai kawai idan aka dauki wani babban mataki.
‘’Daga cikin al’ummar Nijeriya milyan 180, fiye da kashi 75 ne suke zama a karkara wato kauyuka, suna yin bahaya ne wato kashi a waje, wannan kuma shi yasa Nijeriya ta kasance,kasa ta uku a duniya wadda al’ummarta ke yin kashi a waje (sarari). Wannan kuma shi ne yayi sanadiyar mutuwar mutane 45,000 ko wacce shekara a kasar Nijeriya.
‘’Muradin ci gaban da ake sa ran shi ne na shida akan sikelin SDG wanda kuma yafi bada fifiko ne akan akan SDC al’amarin da shi kuma yafi bada fifiko ne akan WASH. Nan da shekara ta 2030 ana bukatar dukkan kasashe su, samu cimma burin samar da ruwan shan tsaftacce ga dukkan al’umma. Hakanan ma nan da shekarar ta 2030 ana bukatar kasashe, su samu damar samar wa kansu miuhalli wanda yake tsaftatacce, da kuma kawo karshen yin kashi a fili.’’ Kamar dai yadda Banda ya bayyana ana kuma bukatar a bayar da kulawa ta musamman ga mata, dakuma ‘yanmata, da kuma wadanda ake ganin ba a cika damuwa da hakkinsu ba.
Yayin da yake bayyana cewar Nijeriya tana kara kokari danagane da samar da ruwan sha a kauyuka, ta bayyana cewar, babban al’amarin da yake damuwarrta shi ne, shine yadda za a dauki matakin tabbatar da tasfatace muhalli, saboda kuwa akwai milyoyin mutane da basu da masan shiga su yi kashi, sai kuma famfuna, kayayyakin da ake wanke hannu da kuma sauran asu abubuwa.
Rashin samar da tsaftataccen ruwa na kara kawo au matsaloli wadanda su kan yi sanadiyar mutuwa, saboda uwar da bata dade da haihua ba, tana iya samar ma shi da cuta, ko ma ta daukar shi kawai, idan bata anke hannunta sosai ba. Ta hanyar kulawa da tsaftace muhalli uwa tana iya ceton jaririnta daga shiga matsala wadda tana iya sanadiyar mutuar shi, da kashi 15.
Rashin kulawa da wanke hannu zai iya shafar makaranta, sboda kuwa idan yaron daya kamu da cutar kwalara, yayi kuma zawo sau da yawa, yana iya samun babbar matsala ta rashin abinci, wanda daga karshe kuma, zai iya shafar hazakar shi dalibin a makaranta, da dai sauran muhimman abubuwa.
Hakanan ma ta bayyana cewar idan ana kulawa da tsfatace muhalli, mata da su kuma ‘yanmatan suna samun mutuncinsu, saboda kuwa su ‘yanmata suna fama da matsala lokacin da suke yin jinin al’ada.
Shi yasa ta kara bayyana ita majalisar dinkin duniya ta hanyar asusun yara anda take da shi, zata ci gaba da bayar da fifiko musamman akan WASH, da kuma wasu suran abubuan kula da lafyar al’umma.
BUGU DA KARI KUMA MAI KULAWA DA TSARIN RUWAN SHA NA KARKARA DA KUMA TSAFTACE MUHALLI, NA MA’AIKATAR KULAA DA ASU BUKATUN MUSAMMAN NA AL’UMMA, NA JIHAR ANAMBRA EZEKWO BIUCTOR, YA BAYYANA CEWAR ITA GWMANATIN JIHAR TA MAIDA HANKALINN TA AKAI.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: