Sulaimon Yusuf, Shugaban kungiyar da ke bayar da kariya kan rushewar gidaje na kasa wato (BCPG) ya nuna damuwarsa kan ci gaba da tashin farashin kayan gina gine a kasar nan.
Ya yi nuni da cewa, matsalar mai yuwa ta janyo yin gine gine da kaya gini marasa inganci wanda hakan zai haifar rugujewar gine gine a kasar.
- Fitar Da Wakokin Da Ke Lalata Tarbiyya Ya Sa Aka Bayar Da Umarnin Kamo Ado Gwanja – Kotu
- Ana Bin Masu Hakar Ma’adanai Bashin Naira Biliyan 3.5 A Jihar Kaduna
Yusuf ya bayyana haka ne a yayin da reshen kungiyar na jihar Legas ya gudanar da yin tattaki a wasu manyan tituna da ke a jihar.
Tattakin wanda kungiayr ta shirya a kwanna baya, taken tattakin shi fadakar d jama’a kan yadda za a magance rugujewar gine gine a kasar nan.
Ya kara da cewa, samun karin hauhawan farashin kayan gine gine kamar irin su Siminti da kayan gyra gini har da kudaden da ake biyan leburori da kuma kwararru masu bayar da shawara a fanin gine-gine, hakan zai iya janyo masu sanar gina gidaje su amfani da kayan gini marasa inganci.
Ya ci gaba da cewa, “Ba da wuri ne za a iya gane illar ba, wanda illar hakan, za ta iya kai wa daga shekara uku zuwa hudu, daidai lokacin da gine-ginen za su fara rugujewa”.
A cewarsa, wannan tattakin zai bayar da dama don a ankara da mutane game da kalubalen da za su iya kunno kai domin a magance akan lokaci, inda ya sanar da cewa, ma’akatar tsare-tsaren tasawiran gina gidaje da kuma ofishin raya birane, akwai rawar da su taka wajen magance matsalar.
Ya sanar da cewa, akwai bukatar su kara kokari domin a tabbatar da ana bin ka’idojin yin gine-gine kuma masu yin gine-gine su tabbatar da suna yin bincike kan ingancin kayan gine- gine na cikin gida.
Ya ce, ya kamata ace dole ne kowacce karamar hukuma daya akalla tana da makarantar bayar da horo ta yin gini wadda matasa za su rinka zuwa don su samu kwarewa a fannoni da ban da ban yin gini.
Ya sanar da cewa, akwai bukatar a samar da shirin daukar nauyi na musamman ga daliban da ke koyon darussan muhallai don a kara masu kwarin guiwa a fannin.