Kungiyar masu kiwata tarwada reshen jihra Edo ta koka kan tsadar man dizil inda suka sanar cewa, tsadar ta man, za ta iya dukusar da sana’ar ta su idan har gwamnati ba ta kawo masu dauki ba.
Shugaban kungiyar na jihar Mista Benjamin Okpere ne ya yi wannan koken a garin Benin, a hirarsa da manema labarai, inda ya yi nuni da cewa, suna fuskantar babbar barazana, saboda tsadar ta man Dizil.
- Nijeriya Ta Yi Barazanar Ficewa Daga Kungiyar ECOWAS
- Gwamnatin Bauchi Ta Amince Da Sabuwar Dokar Kafa Kungiyar ‘Yan Sintiri A Fadin Jihar
Okpere ya bayyana cewa, hada-hadar kasuwancin na tarwada a shekarun baya suna samun ciniki sosai, amma a bana, tsadar ta man Dizil ta jawo musu koma-baya.
Shugaban ya ci gaba da cewa, kamar yadda nake Magana da ku a yanzu, masu sana’ar ba sa samun wata ribar kirki, saboda tsadar ta man Dizil, inda kuma wasu suka dakatar da yin sana’ar, musamman marasa karfi da ke yinta.
A cewar Okpere, wasu masana’antun da ke kiwata tarwada suke kuma yin amfani da man na Dizil, a yanzu sun koma yin amfani da man Fetur, inda suke gudanar da ayyukansu na kiwon zuwa ‘yan awoyi.
Ya kara da cewa, hakan ta janyo wa masu sana’ar rage yawan tarwadar da suke kiwata wa domin sayarwa ga jama’ar da ke da bukata.
Okpere ya kuma koka kan yadda ake samu karin tashin kudaden musaya da kuma yadda farashin masarar da suke ciyar da tarwadar ya tashi, musamman saboda lamarin rashin tsaro da ke addabar Arewacin kasar nan.
Ya yi nuni da cewa, ya zama wajbi gwamnati, musamman gwamtain tarayya da ta samar da mafita kan don magance wannan babban kalubale da masu kiwon tarwadar ke fuskanta.