A ranar Talata ne majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakan shawo kan tsadar rayuwa da ke illa ga ‘yan Nijeriya.
‘Yan majalisar sun yi wannan kiran ne a lokacin da ministocin kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki, Wale Edun; Kasafin Kudi da Tsarin Kasa, Atiku Bagudu; Gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso da shugaban hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS), Zacch Adedeji, suka hallara a gaban majalisar.
- Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
- Shugaban Karamar Hukuma A Kano Ya Yi Murabus, Wani Kuma Ya Fice Daga APC Zuwa NNPP
Zaman ya kasance na biyu don tattaunawa, wanda majalisar ke gabatarwa domin tattaunawa da shugabannin ma’aikatu da hukumomi (MDAs) kan sanin manufofi da tsare-tsaren gwamnati.
‘Yan majalisar sun bukaci shugabannin da su yi bayani kan matakan da CBN, FIRS da ma’aikatu ke dauka dangane da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Da yake jawabi, dan majalisar wakilai, Ahmed Jaha Babawo (APC, Borno) yace, babu wanda yake bukatar cewa, sai an yi bincike domin a tabbatar da cewa, ‘yan Nijeriya na cikin yunwa da bacin rai.
Ya ce, dole ne gwamnati ta dauki mataki musamman ta fuskar tsaro domin ganin al’amura sun yi kyau ga ‘yan Nijeriya.