• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsadar Rayuwa: Yadda Al’umma Suka Yi Sallah Cikin Kunci

bySharfaddeen Sidi Umar, Sokoto and Sulaiman
4 months ago
Tsadar rayuwa

Al’ummar kasa daga Arewa zuwa Kudu sun gudanar da shagalin bukin muhimmiyar ranar Babbar Sallah a cikin mummunan yanayin tabarbarewar tattalin arziki da ya hanawa bukin sallar armashi.

Bukin sallar layya na zuwa ne kwana daya bayan miliyoyin al’ummar musulmin duniya sun yi hawan Arafat, ranar da ta fi kowace rana daraja a cikin ranakun duniya.

  • Saƙon Barka Da Sallah: Tinubu Ya Baiyana Tabbacin Ci Gaban Nijeriya, Da Sauyin Tattalin Arziƙi
  • Abubuwan Da Ba A Fada Ba Game Da Mummunar Ambaliyar Ruwan Mokwa

Sallah Babba wadda ake gudanarwa a kowace ranar 10 ga watan Zul -Hijja a fadin duniya bakidaya rana ce ta musamman da al’ummar musulmi ke yanka dabbobi domin koyi da jagoran Annabawa, manzon tsira kuma shugaban talikai, Annabi Muhammad (SAW)

Al’umma da dama da suka saba yin layya a baya, a bana suna dauke da tambarin matsaloli a fuskokin su domin kuwa layya ta gagare su a dalilin matsin tattalin arziki wanda ke da alaka da tsauraran manufofin tattalin arziki na gwamnatin Tinubu wadanda al’ummar kasa ke kokawa a kai.

Duk da gwamnatoci a dukkanin matakai sun biya albashin watan Mayu amma ma’aikata da dama ba su samu zarafin gudanar da ibadar layya ba domin albashin ba zai wadace su sayen dabbobi da abinci ba.

LABARAI MASU NASABA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

An gudanar da sallah ne bayan da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bayyana ranar Juma’a 06 ga Yuni a matsayin ranar 10 ga watan Zul-Hijja 1446 a matsayin ranar sallar layya kamar yadda ya bayyana a sanarwar da shugaban kwamitin lamurran addinin musulunci kana Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu.

A ra’ayin jama’a da dama ba su da halin sayen dabbobin layya da za su yanka, wasu kuwa sun bayyana cewar ko da suna da halin yin layya to ba ita ce a gaban su ba domin a cewarsu za su shiga cikin gagarumar matsala a gidajen su domin mafi yawa ba su tanadi abincin da iyalansu za su ci ba don haka sayen abinci ne mafi muhimmanci.

Talakawa da daman gaske da kanana da matsakaitan ma’aikata da kananan ‘yan kasuwa sun shaidi sallar layya a wannan shekarar a halin da suke fatar kada Allah ya maimaita domin a ta bakin su ba a taba shaidar sallah a matsin tattalin arziki irin ta wannan shekarar ba.

Tashin gwauron- zabi da dabbobin layya suka yi, hauhawar farashin abinci, tsadar man fetur da halin kuncin da jama’a ke ciki duka abubuwa ne muhimmai da suka taru suka dabaibaye sallar ta hanyar hana mata karsashi.

Gagarumar matsalar tsaro ba dare ba rana daga Borno zuwa Sakkwato, tashin bama- bamai, garkuwa da mutane da kisan gillar da ‘yan ta’adda ke yi wa al’umma ba kakkautawa sun yi matukar tasiri wajen hanawa sallah karsashi.

Rahotanni sun tabbatar da cewar tsananin tsadar da dabbobin layya suka yi ya tilastawa jama’a da dama hakura da yin layya domin abincin da za su ci yana kokarin gagarar su wanda ya zama dalilin da ire-iren wadanda suka samu kudin layya to abinci suke siya wanda shine ya fi muhimmanci.

Auwal Balarabe wani matsakaicin ma’aikaci a Abuja ya bayyana cewar wannan layya ce ta farko a tarihin rayuwarsa da aka yi ba ya da halin yanka dabba wanda a cewarsa ya shiga cikin tarihin da ba zai manta ba a dalilin matsin rayuwa.

Wasu maigidanta a Kano sun bayyana cewar ba za su wahalar da kan su sayen ragon dubu 200 zuwa 250 ba, shanu kuwa sai dubu 500 zuwa miliyan daya don haka suka hakura suka zabi sayen kaji da nama.

Mabambantan al’umma sun bayyana halin rashin da aka fuskanta a wannan shekarar da hauhawar farashin raguna da sauran dabbobin layya ya tilastawa mutane da dama hada kudade domin yin hadakar layya ta hanyar sayen babbarn sa ko saniya wadanda suka kai adadin shekaru biyu na layya.

Wani magudanci Isna’il Abubakar a Sakkwato ya bayyana cewar ragon da ya saya a 2024 a dubu 150 a yanzu sai 260, don haka da shi da makwabta hudu sun hada dubu 800 domin sayen saniya su raba.

Bincike a mabambantan kasuwannin karar dabbobi ya nuna an samu karancin masu sayen raguna, shanu da sauran nau’ukan dabbobi sama da shekarun baya kamar yadda masu sayar da raguna a Abuja, Kano, Bauchi, Kaduna, Neja, Gusau, Sakkwato da Birnin- Kebbi suka bayyanawa manema labarai.

“Ba mu taba ganin sallar da jama’a suka kasa yin tururuwar zuwa sayen dabbobi ba irin wannan shekarar, ko kadan babu ko irin rabin hada-hadar da muka saba samu a shekarun baya.”

A cewar Hassan Mahe ko kadan kasuwar dabbobi a bana ta bambanta da saura domin babu kasuwa, kuma duk da tsadar abincin dabbobi, farashin ya karu ne a dalilin hana shigowa da su daga Nijar da gwamnatin kasar ta yi wanda a kan hakan farashin dabbobin ya ninka.

Baya ga wannan matsalar tsaro wadda ta ki ci ta ki cinyewa gagarumar matsala ce wadda ta hanawa bukin sallah armashi a yankuna da dama da ke fama da matsalar tsaro a kasar nan a dalilin hare- haren ta’addanci.

Haka ma dinbin al’ummar da ke tsugune a sansanin ‘yan gudun hijira ko kadan babu maganar kayatarwar shagalin sallah ko yin layya a wajen su, hasalima ranar sallah kan tuna masu da lokutan baya da suka yi sallah cikin walwala da farin ci a muhallansu kuma a cikin iyalan su.

Kayan abinci kamar shinkafa, masara, gero, dawa, wake, fulawa, man gyada, man-ja da nau’ukan tumatur, albasa, attarugu, tattasai da sauransu sun yi matukar tsada lamarin da tsadar a kullum sai gaba-gaba take yi wanda hakan ya taimaka wajen kara rage armashin sallah domin jama’a da dama ba su da wadatar sayen kayan bukatu.

Maigidanta da dama a tattanawarsu da LEADERSHIP Hausa sun bayyana fatar samun saukin al’amurra ta yadda dabbobi da kayan abinci da na bukatu za su sauko kasa akasin shekaru biyu da suka gabata zuwa yanzu da al’amurra suka tabarbare har jama’a suka shiga cikin kunci maras misaltuwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce
Manyan Labarai

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya
Rahotonni

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

October 4, 2025
Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin
Rahotonni

Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin

October 3, 2025
Next Post
Wajibi A Mayar Da Hankali Kan ‘Yancin Yara

Wajibi A Mayar Da Hankali Kan ‘Yancin Yara

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version