A tarihin Nijeriya, bangaren shari’a bai taba fuskantar matsin lamba ba kamar yadda yake fuskanta a halin yanzu. Tun bayan bayyana sakamakon babban zaben 2023 kallo ya koma kan kotunan da ke sauraron kararrakin zabe, kowa ya zuba na mujiya yana kallon bangaren shari’a ta yadda zai iya warware sarkakiyar da ta dabaibaye kararrakin zabe na yanke hukunci cikin adalci ba tare da tsoro ba ko taimaka wa wani bangare ba.
A lokacin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) ta bullo da tsarin tantance masu kada kuri’a ta na’urar BBAS, lamarin ya rage magudin zabe a Nijeriya, ‘yan Nijeriya sun yi zaton cewa sakamakon zaben zai fi inganci kuma ba zai fuskanci kalubalen shari’a ba. Sai dai kuma ba haka lamarin ya kasance ba.
- Majalisa Ta 10: Zababbun Sanatocin APC Na Arewa Ta Tsakiya Sun Yi Fatali Da Zabin APC
- Sauyin Gwamnati: Wainar Da Ake Toyawa A Jihohin Da ‘Yan Adawa Za Su Karbi Mulki
Jam’iyyun adawar dai sun yi zargin cewa ita INEC a kiyasinta da gangan ta ki yin amfani da bayyana sakamakon zabe na na’urar BBAS ko kin bin ka’idojin zaben shugaban kasa da na gwamna. Wannan ya sanya sakamakon zaben da yawa da ta sanar ya zama masu kawo rigima da suka kai har gaban bangaren shari’a.
Yayin da aka bayyana sakamakon zaben shekarar 2023, jam’iyyu daban-daban da suka yi korafin sun garzaya kotu domin kalubalantar zaben, hanya daya tilo da ‘yan Nijeriya da dama suke bi wajen karbo hakkinsu.
Mutane da yawa suna mamakin ko hukumomin shari’a za su iya tabbatar da adalci tare da yanke hukunci da ke tattare da fatan mutane, kamar yadda aka bayyana a rumfunan zabe.
A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da zababben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, wanda INEC ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a 2023, inda nan take zai fara gudanar da ayyukan shugabancin kasa.
Sai dai da yawan mutane, musamman ma masu adawa da shi, wadanda suke ikirarin cewa sun yi nasara, suna ganin cewa babbar kotun koli, kamar yadda ya faru a kasar Kenya, za ta iya soke zaben idan aka gano cewa an tafka kura-kurai ko magudi.
A lokuta da dama kotun koli ta soke zabukan gwamnonin jihohi daban-daban, amma ba ta taba soke sakamakon zaben shugaban kasa ba, tun a shekarar 1999 lokacin da kasar nan ta dawo mulkin farar huda. Hakan ya sa ayar tambaya kan ko rashin bin ka’ida ne ya sa aka soke zaben gwamnoni ban da na shugaban kasa.
Tare da wasu hukunce-hukunce masu rudani da kotun koli ta yanke, kamar hukuncin baya-bayan nan da ya tabbatar da shugaban majalisar dattawa, Dakta Ahmad Lawan a matsayin dan takarar kujerar sanata a mazabarsa da kuma hukuncin da ya gabata wanda ya bayyana dan takarar gwamna da ya zo na hudu a zaben gwamna a matsayin wanda ya yi nasara, tambayar da ke bakin ‘yan Nijeriya da dama ita ce ko bangaren shari’a za ta iya share wa musatattun mutane da suka shigar da kara hawayansu wajen kalubalantar sakamakon zabe.
Dangane da haka ne kungiyar kwadago ta kasa (NLC) tare da hadin gwiwar kungiyoyin farar hula karkashin kungiyar habaka dimokuradiyar kasa, a ranar ma’aikata ta duniya suka bukaci bangaren shari’a na kasar, musamman alkalan kotun daukaka kara da na kotun koli da ke sauraron kararrakin zabe da su taimaka wajen ceto dimokuradiyya ta hanyar yin adalci ga dukkan koke-koken zaben da aka kawo gabansu.
Gamayyar kungiyoyin da suka hada da kungiyoyin farar hula da na matasa sun yi zargin cewa INEC ta yi wa dimokaradiyyar kasar nan mummunar illa a lokacin zaben 2023.
Wadanda suka kafa kungiyoyin sun hada da Olisa Agbakoba (SAN), Sanata Shehu Sanni, Ambasada Nkoyo Toyo, Farfesa Udenta Udenta, Salisu Mohammed, da Olawale Okunniyi, sun had hannu da karfe da shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), Joseph Ajaero da kuma babban sakataren kungiyar ‘yan kasuwa (TUC), Nuhu Toro, sun hadu wuri daya yayin wani taron.
A cikin jawabin nasa, Ajaero ya yi kira ga bangaren shari’a da su yi amfani da damar yanke hukunci a cikin korafe-korafen da suka taso daga babban zaben shekarar 2023 domin kwato martabar su. Ya ce kungiyar kwadago da abokan huldarta sun shirya a wannan karon domin sa ido a kan yadda ake gudanar da harkokin shari’a.
A cikin jawabin Ajaero mai taken, “Barazana ga dimokuradiyya a Nijeriya da kuma bukatar gaggawa ga ‘yan kasa,” ya ce, bangaren shari’a ya jawo tambayoyi da dama daga wurin ‘yan Nijeriya, inda ya kara da cewa, “idan suka kasa amsa wadannan tambayoyi cikin kankanin lokaci, za mu samar da zauren kunyata ga duk alkalan da suka yanke hukunci, ga alkalan da ke haifar da irin wadannan matsalolin, wanda zai faru nan ba da jimawa ba.”
Ya ci gaba da cewa akwai bukatar kungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA) da dukkanin bangarorin shari’a da su yi magana kan abubuwan da ke faruwa a bangaren shari’a tare da yin tunani a zahiri na warware matsaloli ta yadda bangaren shari’a zai ci gaba da zama wurin da talaka zai iya amsar hakkinsa.
Ajaero ya tunatar da bangaren shari’a da su tuna cewa makomar kasar nan na hannunsu, ya ce, “Ko dai su ceceta ko kuma su sake cin amanarta. Lokacin da suka ce ka je kotu, suna gaya maka cewa nan ne karshen lamari. Waye zai saci doya ya ce a je kotu. A kan wane tunani suke amfani da wadannan maganganun?
“Wannan shi ne matakin ba’a da bangaren shari’a ta kawo, kuma a matsayinmu na ‘yan Nijeriya, dukkanmu muna bukatar mu fito domin ceto bangaren shari’a, in ba haka ba babu bukatar ci gaba da zuwa kotu.”
Ajaero ya kara da cewa NLC ta gano wannan yunkuri ba wai don siyasa ba ne, amma domin ceto kasar nan.
Da yake zantawa da manema labarai a karshen taronsu a dakin taro na Labour House da ke Abuja, sakataren gungiyar TUC, Toyo ya zargi INEC da yunkurin ruguza dimokuradiyya ta hanyar rashin bin dokar zabe da ma nasu dokokin.
Toyo ya bayyana cewa, “Zaben 2023 ya zama wani sabon abu daban, wanda ya kawo cikas ga fatan ‘yan Nijeriya na gudanar da sahihin zabe da kuma hana ‘yan kasa samun ingantaccen shugabanci na siyasa a fadin Nijeriya.
“A bayyane yake INEC tare da hadin gwiwa da wasu ‘yan siyasanmu sun kashe makoman dimokuradiyyar ‘yan Nijeriya da dama, don haka sun je fa harkokin zabe cikin rudani wanda ya saba da alkawarin zaben 2023.
“Abin takaici, galibin ‘yan Nijeriya, musamman matasa wadanda suka yi gwagwarmaya wajen sake dawo da kasar nan mulkin dimokuradiyya sun fara tunanin zabe ya kasance silar kawo cin hanci da rashawa a Nijeriya.
“Saboda haka, a daidai lokacin da mutane da jam’iyyu suka garzaya kotu a matsayin babbar hanyar magance rikice-rikice, muna fatan bangaren shari’a da ta kasance mai yanke hukunci na karshe, za ta tabbatar da cewa ba za a samu batun cin hanci da rashawa ba.
“Muna kira ga alkalan kotun daukaka kara da na kotun koli da su tashi tsaye wajen ganin sun dawo da kwarin gwiwar jama’a kan tsarin da INEC ta yi amfani da ya kawo koma-baya ga dimokuradiyyarmu.”
Sai dai ministan kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo ya caccaki kungiyar kwadagon kan barazanar kunyata alkalan da ke karya ka’idojin shari’a tare da fitar da hukunce-hukuncen da ba suka karya ka’ida kan kararrakin zabe.
Keyamo ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri na tsoratar da bangaren shari’a ta Nijeriya yayin da take shirin fara sauraren karar zaben shugaban kasa, to wata gayyata ce ta ruruta wutar rikici.
A cikin doguwar rubutun da ya yi a shafin Twuta, Keyamo ya ja hankali kan wasu gungun mutanen da ya ce sun kafa kansu a matsayin masu sa ido kan harkokin shari’a dangane da koke-koken zabe da ke gaban kotu.
“Duk wani yunkuri na lalata bangaren shari’a kamar yadda wadancan jaruman suka yi niyyar yin, gayyata ce taso rikici kamar yadda yake faruwa yanzu haka a Sudan. Kamar yadda suke takama da cewa su yi wani yunkuri na daban kuma bai kamata bangaren shari’a ya yi rikitar da su ba, nan ba da jimawa ba za su gane cewa bangaren shari’a ma wata cibiya ce ta daban wadda ba za su iya rikitar da ita ba”, ya rubuta.
Dangane da yadda ake zargin hukumar zabe ta kasa ta gaza tabbatar da sahihin zabe da zai gamsar da masu ruwa da tsaki, yanzu haka bangaren shari’a na fuskantar matsin lamba dagane da yadda za ta warware sarkakkakiyar da ta dabaibaye sakamakon zaben 2023.