Tsakanin Shugaba Buhari Da Talaka Wa Ke Bin Wani Bashi?

Tare da Mu’azu Hardawa 08062333065

hardawamuazu@mail.com

Ganin irin mawuyacin halin da ‘yan Nijeriya suka shiga na wahala ta kuncin rayuwa wadanda suka hada da talauci da rashin aikin yi da karancin mai daga lokaci zuwa lokaci da uwa uba tashin bama bamai a wuraren taruwar jama’a da cikin motoci da ofisoshin hukumomi ko jami’an tsaro da sauran wahalhalu na rayuwa da aka yi fama da su a lokacin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan, wannan ya sa ‘yan Nijeriya neman mafita daga halin da suka shiga ta ko halin kaka.

Don haka ‘yan Nijeriya suka ci gaba da hakuri da nufin tunda lokaci ya yi nisa na mulkin tsohon shugaba Jonathan za su bari har lokacin da za a yi zabe yazo a yi kokarin ganin bayan waccan gwamnati don kowa ya huta.

Haka mutane suka yi ta addu’ah da sadaukar da dukiyar su ta hanyar rokon Allah da tura taimakon kudin kamfen wa shugaban kasa Buhari tare da yin duk wani abu da kowa zai iya don ganin karshen waccan gwamnati da ake ganin ta gaza shawo kan matsalar Boko Haram lamarin da ake ganin idan an ci gaba da haka akwai yiwuwar ba da jimawa ba kowane yanki zai bukaci a bashi cin gashin kasa idan ya so kowa tasa ta fishshe shi ya cigaba da gyara yankinsa.

Ya bayyana tunanin mutanen arewa shi ne Goodluck da mukarrabansa basu da niyyar magance matsalar Boko Haram saboda ganin yadda ake sakaci da ba sojojin da ke wannan yaki abubuwan da suka dace na alawus da kayan aiki da kulawa ta musamman don shawo kan lamarin.

Don haka hatta Yarabawa sun yi nisan tunani kan irin abin da ke faruwa a arewa akwai sakacin gwamnati lamarin da suke ganin idan an gama cinye arewa za a iya komawa kudu maso yamma suma a lalata nasu yankin daga nan kuma ‘yan kudu maso kudu masu mulki a karkashin Goodluck Jonathan sai su bukaci a raba kasa abinda suka jima suna fafutuka, daga nan kurum sai a bar arewa da sauran wuraren da rikici ya lalata sai su zama gina kasa da gyara tunanin mutanen su kurum ya isa babban aiki a gare su.

Yayin da suma wasu ‘yan kudu maso kudu irin su Rotimi Amechi da su Rochas Okorocha da makamantan su ke ganin bai dace ba kasa ta shiga rigima irin ta Boko Haram saboda ba wanda ya san inda za ta tsaya kuma komai na iya faruwa. Ganin haka yasa ire irensu suka hadu da ‘yan kudu maso yamma masu kishi irin su Bola Tinubu da tsohon shugaba Obasanjo da sauran su duk suka marawa ‘yan arewa baya don ganin an sauya gwamnatin shugaba Goodluck don ceto Nijeriya daga halin rashin kwanciyar hankali da ta shiga.

Don haka suka hada kai da ‘yan arewa da suka yi takara da masu fada a ji irin su Atiku Abubakar da su Rabiu Musa Kwankwaso harma da wasu manya a cikin PDP da suka dagawa APC kafa aka yi abin da ya dace don samun nasarar zabar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa, kuma har aka yi nasara kan wannan yunkuri, saboda tunanin kowane Buhari yana da farin jini wurin talaka da shi ne kawai za a ci wannan yaki na kwatar kai.

Duk masu kudi da dama da masu mulki a lokacin sun kosa da abin da ke faruwa na rashin zaman lafiya haka suma talakawa da kullum ran su ke salwanta sun kosa, don haka kowa ya fito aka yi kare jini biri jini da guri’a aka ga bayan gwamnatin PDP a Nijeriya musamman ganin irin tunanin Buhari a kan talaka shine na jin kai da temako da inganta rayuwa da samar da duk wani abu na jin dadi ko kwanciyar hankali da gwamnati PDP ta kasa samarwa. Muhammadu Buhari ya jima yana kamfen da cewa dan Nijeriya na cikin wahala ta gararin rayuwa da sakacin shugabannin PDP ya jefa su, musamman ya yi tunanin bai kamata ace nairar Nijeriya ta lalace ta kai kusan naira 200 ba a ganga da dalar Amurka.

Sai ga ta har 520 a lokacinsa, wanda ko ni na taba hira da shi Buhari baki da baki ya ce ya bar mulkinsa na farko dala bata kai naira uku ba don haka idan ya dawo mulki zai kokarta nemawa naira daraja, a wancan lokacin da muka yi wannan hira dala bata kai naira talatin ba.

Bayan haka kowa ya ga inda yake kuka da hawayensa lokacin kamfe yana cewa bai kamata a sayi litar man fetir sama da naira hamsin ba a Nijeriya don haka idan ya samu mulki zai farfado da wannan farashi na mai ya dawo kasa. Haka kuma kullum maganar Buhari shine matasa da ‘yan Nijeriya basu da aikin yi an bar komai kara zube ya lalace, bayan haka a na zaune cikin yunwa da fatara alhali Allah ya horewa Nijeriya arzikin da kowane danta dai ci moriya wajen sanin Allah ya yi wa kasar sa arziki har yayi alkawarin ba kowane dan kasa maras aiki naira dari biyar tallafi duk wata amma shiru ba labara, duk da sanin kasashen Larabawa da turawa na ba da wannan tallafi tun yaro na cikin uwar sa.

A lokacin yakin neman zabe ya yi ta magana game da inganta hanyoyi da samar da ruwan sha da hasken lantarki har ministan lantarki na yanzu ya na bayyana cewa wata shida kacal ya isa a samar da lantarki a Nijeriya kuma kowa ya ci moriya a farashi mai sauki. Amma yau an wayi gari shekaru uku ba wuta mai inganci, idan an yi kokari anga wannan wata an samu wuta da kima to wani wata sai a ninka wa mutane kudin wuta.

Daga nan kuma sai Allah ya yi ikonsa ya dakile ‘yar wutar da a ka ga an fara samu kuma ba shi zai sai a hankalta a rage kudin ba. Har ma an kai ga yanzu wata mita ake dorawa a saman pol wacce idan ka zuba dubu biyar baya kai mako a matsakaicin gida mai dakuna hudu ko biyar, da mutane suka koka sai suka ce ai wuta ba shinkafa ko masara ba ne wanda zai iya ya biya wanda ba zai iyaba ba dole  ya zauna a duhu, wannan shine mulkin Baba Buhari wanda idan na rantse da cewa da mutane sun san za su fiskanci irin wannan matsala a lokacin yakin neman zabensa da yawa ba za su zabi wannan gwamnatin ba.

Irin wannan isgilisanci da tozarci an yi shi a kamfanin sadarwa na NITEL shekarun baya inda su ke cewa wayar tarho naira dubu hamsin layi idan mutum yana so a sa masa idan ba zai iyaba dama waya ba kayan talaka bane, ana tafiya sai Allah ya kawo wayar salula inda wayar dubu daya tsohuwa da layin kyauta a ciki sai ka kira ingila minti hudu da naira dari, ka gama ka jefata a aljihunka ba ruwanka da igiyar da NITEL ke sawa a gida, ikon Allah kenan da haka karshen NITEL ya zo a Nijeriya.

Allah ba inda bai iyaba alamu na nuna za a wayi gari NEPA ta iya zama labari saboda yadda ake kawo fasaha irin ta amfani da hasken rana ko iska a wannan zamani ta yadda idan Allah ya ga dama zai iya karya su nan take kowa ya saya ya dora a kan rufin gida dare da rana ya ga haske kamar yadda masu kudi suka far har zuwa lokacin da ake ganin fasahar za ta iya rage yawan batiran da za a rika amfani da su domin adana makamashin da rana ta caza.

Game da harkar man fetir shugaba Buhari ya yi wa ‘yan kasa alkawarin komai zai inganta fiye da zaton kowa wajen samun albarkatun man fetir, amma yanzu an wayi gari duk da karin kudin man fetir da ya yi ba man har an dawo yanzu ana tunanin karin kudin man fetir. Kasancewar lokacin da ya kara farashi daga 87 zuwa 145 wasu yan kasa, musamman kungiyar kodago sun nuna tirjiya amma sai talakawa suka ce ba damuwa baba Buhari ne ko mai zai kai naira dubu biyu sun san ba damuwa wataran zai sauka.

Akwai talakawan da ke cewa ko zamu ci kasa sai Baba Buhari, kuma har yau akwai masu wannan ra’ayi na tsammanin wa rabbuka da nufin rayuwarsu za ta inganta nan gaba.

Amma maimakon rayuwar ta inganta an kai wani matsayi da rayuwar kara tsanani take yi inda duk wani talaka da ke zuwa asibitin gwamnatin tarayya  yanzu bai isa zuwa ba saboda yadda aka ninninka kudin ayyukansu haka makarantun gwamnatin tarayya suma an ninninka. A kullum tinanin gwamnati shine ina za ta tatso talakan kasa ta samu kudi yadda hatta masu gidajen biredi ko gidan block ko gidan ruwa da kanana da manyan kamfanoni a kullum damun su a ke yi da kawo kudi ko na haraji ko na wasu abubuwa inda an kai wani matsayi yawancin kamfanoni manya da kanan duk sun rufe basa iya aiki kuma babu wani tallafi da gwamnati ta mu su, don inganta ayyuka ko da kuwa na yafe musu haraji ne don ya kasance sun kama aiki mutane sun samu abin yi.

Haka duk wani dan kasuwa babba ko karami kamfani babba ko karami a kullum rufewa suke yi saboda rashin ciniki da rashin jari da tatsar haraji da sauran wahalhalu da a kullum hukumomi kala kala ke shigowa da rasidin neman kudin shiga alhali ba masu saye ko abokan hulda da za a samu kudin biyan wuta da ma’aikata da sayen kayan aiki da makamantan su.

Gwamnati a kullum cewa take yi za tab a da rancen gyara masana’antu ko na koyon sana’a ko jari ko noma, amma idan an kawo sai a taras a rubuce kurum batun yake fadane ba cikawa, saboda ka’idojin da a ke gindayawa cikin mutum dari ko kamfani dari dakyar ashirin su cika ka’ida. Kuma idan an bayar sai ya kasance an bayar da hannun dama an kwace da hannun hagu don haka daga karshe sai a tashi a tutar babu, illa manyan ‘yan siyasa da ke gindin magani ko gwamnoni ko ministoci sune da yaransu za su ci moriyar duk wani abu da aka kawo da nufin sun kafa kamfanoni amma sai an je wurin aga ba komai wannan shine Nijeriya a hannun masu gaskiya.

Kudirin gwamnatin Buharine a inganta Noma kowa ya cid a bakinsa an rufe kan iyaka babu shigowa da shinkafa ko duk wani nau’in abinci da nufin kasa ta ciyar da kanta. Amma abin mamaki duk wani kudi da a ke cewa za a bayar don wannan aiki talakan da ake yi dominsa baya sanin me a ka yi ko me za a yi idan ma ya sani an bashi wani abu sai ka iske bai wuce abin da zai ciyar da bakinsa ya je gona bane illa iyaka lissafine na ‘yan book a takarda.

Kuma idan ance kowa ya koma gona mutane nawane manoma, wanda ke Abuja ko Lagos ko Kaduna ko Kano ko Ibadan ko Kalaba da sauran yankin dab a a noma yaya za su ci wannan moriya. Hatta a arewan Jihohin Borno da Yobe da Adamawa yawanci basa iya noma saboda tashin hankali.

Kuma idan mutum yana da gonar bashi da kudin masu aiki bashi da kayan aiki wani idan ya samu irin da zai shuka akwai bukatar ya gyara ya ci saboda yunwa. Wanda suka fara suka daure sai ka iske yabanya ta yi ba kudin taki ba kudin noma ko maganin shuka haka abin zai lalace.

An sani Buhari ba zai yi rowan kudin ko kyauta wa mutane ba, amma wasu aikin gwamnati suke yi mafi karancin albashi dubu 18 kudin buhun shinkafa to yaya za su cike gibin cefane da sufuri da kudin makaranta da sauran gararin rayuwa.

Bayan haka wani bai iya komai ba sai aikin gwamnati soja  ko dan sanda ko mai aikin ofis albashi bai kai ciyar da bakisa shi kadai ba ballantana iyalen sa. Don haka kowa ya sani ta kowace hanya zai nemi rayuwa ko da cin hanci ko cin kafa ko duk wata hanya day a ke ganin itane za ta fidda shi saboda dole duk ran da Allah ya halitta sai ya ci ya rayu.

Bayan haka arewa sune suka yi uwa da madaukiya wajen kawo gwamnatin Buhari, amma an wayi gari duk kan iyaka kusan kofa dubu da ke arewa duk an rufe sub a mai shiga da fita da duk wata harka ta arziki walau mota ko kayan amfanin yau da kullum ko kayan abinci. Alhali wadanda ke kudu masu mashigin ruwa an bude musu hanya suna shiga suna fita suna walwala inda ransu ke su kasuwancin sun a gudana.

Amma arewa duk da cewa an san kowane mutumin da garinsu ke kan boda wato iyakar kasa to abincin a wurin yak eta hanyar saya da sayarwa ko fiton kayak o na motoci ko gyaran mota ko wankewa da makamantansu, amma an rufe kirif don haka tunda rayuwa ta zama dole wasu matasan da ke cit a irin wadannan harkoki sun koma fashi wasu sun zamo barayi wasu sun zamo masu garkuwa da mutane wasu sun koma ‘yan luwadi ko kawalci mata sun koma mazinata ga wanda ke da fasalin a ganta a sota wasu kuma sun koma cikin tsananin wahala da yunwa da talauci amma duk kukan da ake yi sai a ce an sani gyara ake yi bamu san yaushe wannan gyara zai amfani talakaba.

Duk duniya babu abin day a fi karfin gwamnati kuma duk duniya kowa ya sani ana shiga a fita ta ruwa da sama da kasa, kuma kowace irin na’ura gwamnatin Nijeriya na iya saya ta saka don tantance mai shiga da fita, yadda a halin yanzu ‘yan arewa da suka yi gwagwarmayar zabe an jona musu talauci mai tsanani da rashin hanyar ciyar dab akin su ko yin nomar yadda ya dace, don haka an wayi gari wannan sauyi bai yi tasiri wa mutane ba.

Kuma abin takaici duk wadanda aka ba mukamai cikin wannan gwamnati basu damu da temako ba saboda gani suke yi kamar ba za su sake dawowa ba don haka Tarawa kurum suke yi da nufin kar su tsiyace alhali lamarin na Allah ne, kuma duk cikin su babu wani mai kafa kasuwanci akasari don wani ya amfana.

Sanin kowane mutane da dama sun dauki gwamnatin Buhari a matsayin tudun muntsira na wahalhalin da suke sha amma sai aka samu akasi ba sauki ciwon arne kullum wahala sai kara gaba ta ke yi rayuwa sai salwanta suke yi ta hanyoyi dabam dabam kama daga yunwa ko rashin magani ko rashin aiki ko rashin kwanciyar hankali da makamantan su.

Abin mamaki duk wata manufa da wannan gwamnati ta sa gaba idan an ce ta yi tsauri a bibiye ta sai ace gyara ake yi muna sane ba a san yaushe za a gama wannan gyara ba ko sai an ji yawancin mutanen kasa a lahira sai Allah shine ya barwa kansa sani.

Kuma abin mamaki har yanzu suma talakawa wasu basa yiwa shugaba Buhari adalci ta hanyar fitowa su bayyana matsalolin da suke fuskanta da irin radadin da suke sha saiko su ce Baba Buharine gyara yake yi duk na gindinsane basa kaunar gwamnatinsa ke kawo masa cikas, anya da abin da ya fi karfin gwamnati ko wanda ya fi karfin gwamnati komai lalacewarta.

Don haka ko me ake ciki lokacine zai nuna saboda saura shekara daya tak ayi zabe kuma wanda suke kan mulki sun fi masu neman kwacewa son su koma duk da irin wahalar da suke sha, don haka bamu san yaushe gwamnati za ta biya talaka bashin day a ke binta ba ko kuma yaushe talaka zai biya gwamnatin Buhari bashin da ta ke binsa na yunwa da taluci da kuncin rayuwa, da ya shiga ba.

Yanzu dai lokacine zai yi bayani fatarmu shine Allah ya kawo karshen wahalar da ake ciki, don shi mutum idan wahala ta  yi yawa zai nemi rayuwa ta ko halin kaka ko da girma ko da arziki da fata Allah ya mana jagora.

 

 

Exit mobile version